Korar Sanusi II daga Kano da tsaresa: IGP ya bukaci kotu da ta yi watsi da karar

Korar Sanusi II daga Kano da tsaresa: IGP ya bukaci kotu da ta yi watsi da karar

Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bukaci babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta yi watsi da karar tubabben sarkin Kano, Lamido Sanusi, da ke kalubalantar hakkokinsa da aka take bayan sauke rawaninsa.

A sukarsa ta faro, sifeta janar na 'yan sandan ya musanta cewa kotun bata da karfin ikon jin wannan karar.

A ranar 9 ga watan Maris ta 2020, gwamnatin jihar Kano ta tube rawanin Sarki Sanusi sannan jami'an tsaro suka fitar da shi zuwa Abuja.

Daga bisani an mayar da shi garin Awe na jihar Nasarawa inda aka tsareshi a wani gida har zuwa ranar 13 ga watan Maris. Daga nan ne ya samu hukuncin gaggawa daga kotu inda ta bukaci a sake sa.

A wata kara da Sanusi ya shigar ta bakin lauyansa, Lateef Fagbemi (SAN), ya ce korarsa da kuma tsaresa da aka yi sun take hakkinsa na 'yancin zuwa inda yaso da sauransu.

A yayin kalubalantar karar, sifeta janar na 'yan sandan ya musanta korafin da Sanusi ya bada na cewa an take hakkinsa bayan saukesa daga kujerar sarautar Dabo. Ya ce Kano ne ya kamata ya shigar da karar ba Abuja ba.

Tube rawanin Sanusi II: IGP ya bukaci kotu da ta yi watsi da kara
Tube rawanin Sanusi II: IGP ya bukaci kotu da ta yi watsi da kara. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda Gwamnan PDP ya sha 'ihu barawo' daga jama'arsa

Ya ce, "Zargin take hakkin mai shigar da kara bayan sauke masa rawani, duk zai iya tasiri ne a babbar kotun jiha.

"Sanannen abu ne idan aka ce komai ya faru ne a cikin jihar Kano, inda mai karar aka tube masa rawani a matsayinsa na Sarki kuma aka kai shi Abuja inda aka karasa da shi zuwa jihar Nasarawa.

"A bangarenmu, za mu ce shigarsa Abuja kawai wucewa aka yi amma a kan hanyar zuwa jihar Nasarawa yake. Abuja ba za ta taba zama inda aka danne masa hakkinsa ba don babu abinda ya faru."

IGP ya kara da cewa, tube rawanin wanda ya kai ga korar basaraken daga jihar, za a iya shari'ar a babbar kotun jiha ba ta tarayya ba.

Amma kuma, Sanusi ya ce ba karar tube rawaninsa ya kai ba. Yadda ta karfi da yaji da aka fitar da iyalansu daga fadar kuma aka koresa daga Kano tare da tsaresa ne yake kara.

Ya musanta cewa an take hakkinsa amma ba a Kano kadai ba don an shiga jihohin Kano, Abuja da Nasarawa.

Mai shari'a Chikere ya saka ranar 20 ga watan Oktoba don sauraron shari'ar

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel