Kotu ta Tasa Keyar Uwa Da Danta Kurkuku Bisa Satar Kayan Kamfanin Miliyoyin Naira

Kotu ta Tasa Keyar Uwa Da Danta Kurkuku Bisa Satar Kayan Kamfanin Miliyoyin Naira

  • Kotu ta aika wata uwa, Lola Disu da danta Ahmed Disu gidan yari bisa zargin hada baki da sace kayan kamfanin Uccas Resources Ltd da suka hada da fanka, kujeru da sauransu
  • An zargi mutanen biyu da wasu sun hada baki wajen sato kayan har da buga takardar kotu na bogi dake nuna cewa an kwace wadannan kaya daga kamfanin
  • Bayan karanta musu tuhumar da ake musu, uwa da dan sun musanta inda nan take Mai Shari'a Abimbola Awogborota ta bayar da umarnin aikewa da su fursun zuwa ranar Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos- Wata uwa da danta sun gamu da fushin hukumar bayan gurfanar da su gabanta da zargin satar kayan kamfani da suka tasamma miliyoyin Naira a jihar Lagos.

Kara karanta wannan

Wa zai zama Sarkin Kano? Abin da kotuna 2 suka ce game da makomar Sanusi II da Aminu

Kamfanin Uccas Resources Ltd ne ya gurfanar da Lola Disu da danta, Ahmed Disu gaban kuliya bisa zargin satar kayan akalla N122m.

Gidan yari
Kotu ta aike da uwa da danta gidan yari bisa zargin sata Hoto: Caspar Benson
Asali: Getty Images

Leadership News ta wallafa cewa da farko 'yan sanda sun shaidawa kotu yadda mutanen suka yi batan dabo lokacin da ake nemansu ruwa a jallo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta sanya ranar shari'ar uwa da 'da

Bayan laifin satar kayan kamfani, ana zargin Lola Disu da danta Ahmed Disu da laifin samar da takardar kotu ta bogi.

Takardar na dauke da rubutun cewa 'kotu ta kwace wannan kadarar', kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

Wasu daga kayan da ake zargin mutanen biyu da sauran abokansu sun sace ya hada na'ura mai kwakwalwa, fankoki, tebur, kujeru, na'urar sanyaya daki da sauransu.

Mai Shari'a Abimbola Awogboro ta tura su gidan yari kafin ranar 29 Mayu domin sauraren bukatarsu na beli.

Kara karanta wannan

Kano: An shiga ɗimuwa bayan jin harbe harbe a fadar da Aminu Ado Bayero yake

Kotu ta yi hukunci kan dambarwar sarauta

A baya mun kawo muku labarin cewa babbar kotu da ke zamanta a Kano ta haramtawa jami'an sojoji da 'yan sanda yunkurin fitar da Malam Muhammadu Sunusi II daga gidan sarautar Kano.

Ana ta samun hukunce hukuncen kotu kan dambarwa masarautar Kano da aka fara tun makon da ya gabata bayan rushe masarautun da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.