Hukumar Kwastam Ta Dakile Yunkurin Shigo da Fetur da Abinci Daga Makwabtan Najeriya

Hukumar Kwastam Ta Dakile Yunkurin Shigo da Fetur da Abinci Daga Makwabtan Najeriya

  • Hukumar hana fasa-kwauri ta kasa ta bayyana nasarorin da ta samu wajen dakile shigo da haramtattaun kaya Najeriya ta iyakar Seme ciki watanni uku
  • Shugaban hukumar a yankin Timi Bomodi ya ce sun dakile yunkurin shigo da akalla buhunan shinkafa 10 da litocin man fetur 373,440 da wasu kayan
  • Ya kiyasta cewa kudin haramtattun kayan da hukumar ta kama domin kada a shigo da su Najeriya ya kai N840m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos-Jami'an hukumar hana fasa-kwauri ta bayyana dakile yunkurin shigo da buhunhunan shinkafa 'yar waje akalla 6,467 da litar mai 373,440 ta iyakar Seme.

Kara karanta wannan

Nijar da wasu kasashen Afrika sun sha wutan $51m sun ki biyan Najeriya kudin lantarki

Wannan ya zo daidai da tireloli 10 ke nan na shinkafar da wani kasungurmin dan fasa-kwauri da ya saba safarar kaya ya yi yunkurin shigowa da su.

Hukumar kwastam
Hukumar kwastam ta kama tirelar shinkafa 10, man fetur da wasu kaya a iyakar Seme Hoto: Nigeria Customs Service
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa shugaban hukumar da ke kula da yankin, Timi Bomodi ya shaidawa manema labarai cewa dakile shigo da haramtattun kaya sau 474.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwastam ta kama masu fasa-kwauri 18

Hukumar hana fasa-kwaurin Najeriya ta dakile yunkurin shigo da litocin man fetur 373,440 daga kasar Benin zuwa Najeriya.

Leadership News ta wallafa cewa haka kuma jami'an hukumar sun kama tirelolin shinkafa guda 10 da aka so yin fasa-kwaurinsu ta iyakar Seme.

Mutane 18 shugaban hukumar, Timi Bomodi ya ce sun kama wadanda ake zargi da hannu cikin safarar haramtattun kayan a cikin watanni uku.

A karin bayaninsa, hukumar ta hana shigo da tayar mota da dabbobin dawa, sai tabar wiwi da sauran haramtattun kaya da gwamnati ta hana shigo da su.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kinkimo namijin aikin da zai amfani mutane miliyan 30 a Najeriya

Kwastam ta fara sayarwa talakawa abinci

A baya mun kawo muku labarin cewa shugaban hukumar kwastam na kasa, Adewale Adeniyi ya ce za su fara sayarwa 'yan Naeriya shinkafa domin rage yunwa a kasa.

Shugaban ya bayyana haka ne a gaban majalisa yayin taro kan samar da dabarun wadata kasa da abinci da ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ya hada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel