Sojoji Sun Cafke Soja Bisa Zargin Sace Harsasan Yaki da 'Yan Ta'adda a Borno
- Jami'an rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wani soja bisa zargin satar harsasai masu tarin yawa a jihar Borno
- Sojojin na rundunar Operation Hadin Kai tare da ƴan sa-kai na 'Civilian Joint Task Force' (CJTF) sun cafke sojan mai suna Francis Bako a tashar mota
- Sojan yana kan hanyarsa ta zuwa Kaduna ne lokacin da jami'an tsaron suka yi nasarar cafke shi ɗauke da harsasai 602 na musamman masu kaurin 7.62mm
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai dake Maiduguri a jihar Borno sun cafke wani soja mai suna Francis Bako bisa zargin satar harsasai.
Sojojin sun cafke jami'in tsaron ne tare da haɗin gwiwar dakarun sa-kai na CJTF.
A cewar Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, jami'an sirri na sojoji sun cafke sojan ne a tashar mota.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ina aka cafke sojan?
Majiyoyi sun bayyana cewa sojojin sun cafke Francis Bako ne a tashar mota ta Kano da ke cikin birnin Maiduguri bayan sun samu bayanan sirri.
Sojan wanda yake aiki a Mallam Fatori, yana kan hanyar zuwa Kaduna ne lokacin da aka yi caraf da shi.
Bayan an cafke shi, an same shi ɗauke da harsasai 602 na musamman masu kaurin 7.62mm.
Wata majiya ta bayyana cewa:
"A halin yanzu sojan yana hannun sojoji don ci gaba da ɗaukar mataki na gaba."
Sojoji sun sheƙe ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun runduna ta ɗaya ta sojojin Najeriya da ke aiki a Kaduna sun kashe ƴan ta'adda bakwai a ƙauyen Udawa da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar.
Dakarun sojojin sun samu wannan nasarar ne a wani aikin sintiri da suka gudanar a kan hanyar Udawa-Kurebe.
Sojojin sun kuma ƙwato makamai da dama daga hannun ƴan ta’addan da suka haɗa da wata jigida ta bindigar AK-47 da babu komai a ciki, babbar bindiga ɗaya, harsashi shida da sauran makamai masu hatsari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng