Gwamnatin Kaduna Ta Daura Damarar Yakar Yan Ta'adda, Ta ba Jami'an Tsaro Tallafi

Gwamnatin Kaduna Ta Daura Damarar Yakar Yan Ta'adda, Ta ba Jami'an Tsaro Tallafi

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta dauki matakin taimakawa jami'an tsaro dake aiki a jihar domin dakile hare-haren 'yan bindiga da sauran miyagu
  • Gwamnan jihar Uba Sani ne ya kaddamar da ababen hawa, wanda ya hada da motoci 150 da babura 500 a wani bangare na cikarsa shekara kan mulki
  • Ya bayyana takaicin yadda aka rasa wasu jami'an tsaro da ke yakar ta'addanci a jihar, tare da alkawarin ci gaba da basu gudunmawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna-Gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da motoci 150 da babura 500 domin rabawa ga jami'an tsaro dake yaki da ta'addanci a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta binciki yadda Buhari ya jinginar da filayen jirgin sama

Gwamna Uba Sani da ya kaddamar da ababen hawan a yau Talata ya ce yana sane da yadda jami'an ke fuskantar matsalar sufuri wajen yakar miyagu.

Jihar Kaduna
Gwamnatin Kaduna ta raba motoci, babura ga jami'an tsaro Hoto: Kaduna State Vigilance
Asali: Facebook

Leadershsip News ta wallafa cewa gwamnan ya roki 'yan majalisa su gaggauta amincewa da samar da 'yan sandan jihohi domin hakan za taimaka sosai wajen yakar ta'addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Mun jinjinawa jami'an da suka rasu,' Uba

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya bayyana takaici kan yadda wasu jami'an tsaro a jihar suka rasa rayukansu yayin kare mazauna kasar nan.

Ya ce su na sane da irin kokarin da jami'an suke yi wajen tabbatar da tsaro a sassan jihar Kaduna da 'yan bindiga ke yawan kai wa hari, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin sanya sunan marigayi Laftanar Kanal AH Ali da 'yan ta'adda suka kashe a kudu maso kudancin kasar nan a dakin taro dake ma'aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida.

Kara karanta wannan

Rikicin Kano: Abin da Sarki Sanusi II ya faɗawa manyan jami'an tsaro a fadarsa

Yan ta'adda sun sawa manoman Kaduna sharuda

A baya mun kawo muku labarin cewa rashin tsaro a jihar Kaduna na kara ta'azzara yayinda 'yan ta'adda suka sanyawa manoma sharudda kafin yin aiki a gonakinsu.

'Yan ta'adda sun bayyana cewa duk manomin dake son yin aiki a gonarsa cikin kwanciyar hankali ya nemo kudin fansar kansa na N100,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.