Yunwa, Fatara, Aikatau da Rashin Tsaro: Kadan Daga Kalubalen Yara a Najeriya, UNICEF
Yayin da duniya ke bikin ranar yara ta duniya, akasarin yara a Najeriya ba za su iya bikin wannan rana ba duba da kangin rayuwa da suke ciki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kano - An gano cewa yaran kasar nan na cikin jarrabawar rayuwa, ba kamar takwarorinsu dake sassan duniya ba, musamman kasashen da suka ci gaba.
Akalla, akwai wasu bangarori hudu da yara a Najeriya suka fi fuskantar kalubale wanda ke janyo musu nakasu wajen samun ingantacciyar rayuwa.
Kalubalen da yaran Najeriya ke ciki:
1. Mace-macen kananan yara
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akalla yara 800,000 ne ke mutuwa a Najeriya kafin su kai shekara biyar saboda cututtukan da za a iya magancewa ciki har da shan inna, malaria da farankama.
Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta bayyana cewa malaria na daga abin da ke hallaka yara 'yan kasa da shekaru biyar a duniya.
Kuma Najeriya ce ke da 31% na adadin wadanda zazzabin cizon sauro ke ajalinsu a fadin duniya, mafi akasarin su yara ne.
2. Rashin Ilimi
A rahoton da Daily Trust ta wallafa, miliyoyin yara a Najeriya ne ba su samun damar zuwa makaranta ballantana su samu ilimi.
Hukumar kula da tarihi da al'adu (UNESCO) ta ce Najeriya ta fi kowacce kasa yara marasa zuwa makaranta, wanda adadinsu ya kai miliyan 10.5.
An danganta rashin zuwan yara makaranta da talauci, al'ada, sai rashin karancin kayan koyo da koyarwa.
3. Rashin Tsaro
An gano cewa rashin tsaro a Najeriya na jefa yara cikin mawuyacin hali ta fuskoki da dama, inda hakan ke taba lafiyar kwakwalwarsu.
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta gano cewa akalla mutane miliyan 1.9 ne suka rasa matsugansu a Najeriya saboda rashin tsaro.
Hukumar ta kara da cewa mafi yawan wanda abin ya shafa yara ne kanana da ke fadawa maraici bayan kashe iyayensu da 'yan ta'adda suka yi.
4. Aikatau da cin zarafi
Hukumar kidaya ta kasa ta bayyana cewa kaso 60% na yara a Najeriya na fuskantar cin zarafi ko yaya ne kafin su kai shekaru 18 da haihuwa.
Daga irin cin zarafin da yara ke fuskanta akwai duka, zagi, fyade da kuma bautarwa.
Gwamnati ta yi alkawarin inganta rayuwar yara
A baya mun baku labarin cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin inganta rayuwar yara a kasar nan.
Ya dauki alkawarin ne yayin da ake bikin yara ta duniya, inda ya ce yara su ne ginshikin al'umma saboda haka suna bukatar kulawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng