Sarautar Kano: Kamar Sanusi II, Shi Ma Aminu Bayero Ya Yi Zaman Fada a Nassarawa

Sarautar Kano: Kamar Sanusi II, Shi Ma Aminu Bayero Ya Yi Zaman Fada a Nassarawa

  • Sarkin Kano na 14, Aminu Ado Bayero, ya karbi mubaya'a daga wasu hakiman Kano da ake zargin sun ki yin biyayya ga Muhammadu Sanusi II
  • An ruwaito cewa a yayin da Aminu Bayero ya ke zaman fada a Nassarawa, a daidai lokacin ne shi ma Sanusi II ya ke zaman fada a Kano
  • Akalla dai hakimai 40 cikin 65 ne muka ruwaito suka tabbatar da mubayi'ar su ga sabon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Rahotanni na nuni da cewa yanzu haka Aminu Ado Bayero, tsohon Sarkin Kano, yana karbar gaisuwa daga hakimai a cikin fadar Nassarawa.

Haka zalika shi ma Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya yi zaman fada tare da hakimai a yau Lahadi a fadar sa ta Kano.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Jerin hakimai 40 da suka yi mubayi'a ga Sanusi II, 25 sun yi jinkiri

An samu rarrabuwar kan hakimai a masarautar Kano
Rikicin sarauta: Sanusi II, da Aminu Bayero sun yi zaman fada a Kano da Nassarawa. Hoto: @Waspapping
Asali: Twitter

Jaridar TheCable ta fahimci cewa hakimai da suka yi wa Aminu Bayero mubaya’a ba sa biyayya ga Sarki Sanusi II.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano dai ta fada cikin rikicin sarauta tun bayan da aka mayar da Sanusi II a matsayin sarki ranar Alhamis.

Gwamna ya sa a kama Aminu Bayero

A ranar Asabar ne Bayero ya koma Kano inda ya samu tarba daga dandazon magoya bayansa tare da yi masa rakiya zuwa fadar Nassarawa.

Sai dai kuma nan da nan gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya ba da umarnin a kama Aminu Bayero saboda yunkurin "tayar da zaune tsaye".

Amma dai rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi biris da wannan umarni na Gwamna Yusuf inda ta bayyana cewa za ta yi biyayya ga umarnin babbar kotun tarayya.

Babbar kotun tarayyar karkashin jagorancin Mai shari'a Liman ta dakatar da Abba daga aiwatar da dokar da ta rusa masarautun jihar Kano.

Kara karanta wannan

"Ka hakura da zaman Kano": Kungiyar Arewa ta ba Sarki Aminu shawara bayan an tsige shi

Sarakuna na zaman fada 2 a Kano

Duk da wannan umarnin na kotun, gwamnan jihar ya mika takardar nadin sarki ga Muhammadu Sanusi II tare da mayar da shi gidan sarautar Kano.

Tabbatar da zaman sarki a Kano da kuma zaman fadar Aminu Bayero a Nassarawa ya jawo jami'an tsaro sun yi ganawa da bangarorin da rikicin ya shafa.

Amma za a iya cewa har yanzu takaddamar ba ta kare ba tunda dai Aminu Bayero da Sarki Sanusi II na ci gaba da gudanar da zaman fada a wurare daban-daban.

Hakimai 40 sun bi Sarki Sanusi II

A wani labarin, mun ruwaito cewa akalla hakimai 40 cikin 65 ne muka ruwaito suka tabbatar da mubayi'ar su ga sabon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Wannan na nufin cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II ya samu goyon bayan mafi rinjaye hakiman da ke a jihar, yayin da ya shirya gudanar da mulki a masarautarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.