Kuskuren Majalisa Wajen Rusa Sarakunan Kano Inji Hadimin Tsohon Shugaban Majalisa

Kuskuren Majalisa Wajen Rusa Sarakunan Kano Inji Hadimin Tsohon Shugaban Majalisa

  • Tsohon hadimin shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Hassan Cikinza Rano ya ce majalisa ta tafka kuskure kan dokar rushe masarautu
  • A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce majalisa ba ta bi tsarin da ya dace wajen nada Malam Muhammadu Sanusi II sarkin Kano ba
  • Tsohon mai bawa shugaban majalisar dokokin Kano shawara ya ce dole sai an samar da sabuwar doka kafin nadin Malam Sanusi II a matsayin Sarki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, tsohon hadimin shugaban majalisar dokokin jihar, Hassan Cikinza Rano ya bayyana cewa an tafka kura-kurai.

Kara karanta wannan

Sarki 2 a lokaci 1: Lauyoyin Kano sun fitar da jawabi ganin an jibge jami'an Sojoji

'Dan siyasar ya ce ko kadan majalisar ba ta bi hanyar da doka ta tanada wajen nada Malam Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon sarkin Kano ba.

Sarautar Kano
Tsohon hadimin Shugaban majalisa a Kano, Hassan Cikinza Rano ya ce an yi kuskure wajen nada sabon sarki Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na facebook, tsohon hadimin na ganin akwai wasu abubuwa da dole sai majalisar ta yi gabanin nada sabon sarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sarakunan Kano suna nan" - Rano

Hassan Cikinza Rano na ganin babu yadda za a yi majalisar Kano ta iya tabbatar da tsige sarakunan da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta nada.

A sakon da ya wallafa a facebook, ya rubuta cewa:

"Tsarin Shine Idan Za'a Rushe Doka To Sai an kirki wata dokar, Lokacin da mukazo Yan Majalisa na wancan lokacin sun rushe dokar Masarautu na baya Suka kirki sabuwa 2019. Zan binciko muku dokar."

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Lauya ya lalubo lungun da Abba ya saba doka wajen maido Sanusi II

"Sukuma da sukazo maimakon su kirki doka sai sukace sun ruguje. sukace wai a koma Bayan 2019 Itakuma Bayan 2019 Babu Wata Doka Kaga kenan Babu Wani Amendment Na Rusa Masarautu. Indai Akwai KOTU WALLAHI SARAKUNANMU ZAMA DARAM DAM. Kuma Yanda Na Gaya muku Dinnan Haka Zancenan Yake."

Sarkin Gaya ya mika wuya

A baya mun kawo muku labarin cewa tu66a66en sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim AbdulKadir ya bayyana cewa ya karbi kaddara.

Wannan na zuwa ne yayin da sarki na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ja daga tare da kin amincewa da tunbuke rawaninsa da gwamnati ta yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.