Rikicin Masarauta: Zanga Zangar Adawa da Nadin Sarki Sanusi II Ta Mamaye Kano

Rikicin Masarauta: Zanga Zangar Adawa da Nadin Sarki Sanusi II Ta Mamaye Kano

  • Wata sabuwar zanga-zanga ta sake barkewa a jihar Kano kan batun mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano
  • Masu zanga-zangar suna kira ne da a tsige Sanusi II tare da mayar da Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano
  • Suna zanga-zangar ne a kan titunan karamar hukumar Gaya da kuma Nasarawa inda Aminu Ado Bayero yake zaman fada

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Zanga-zanga ta barke a wasu sassa na Kano a ranar Lahadin nan kan matakin da gwamnatin jihar ta dauka na maido da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

A Gaya da Nasarawa inda aka gudanar da zanga-zangar, al’ummar garuruwan sun mamaye tituna domin nuna adadawa da dawo da Sanusi II kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Zanga zanga ta barke a fadar masarautar Gaya da majalisa ta rusa

Zanga zanga ta barke a Gaya, Nasarawa kan nadin sabon sarki a Kano
Kano: Mutane a Nasarawa da Gaya sun nuna adawa da mayar da Sanusi II kan karagar mulki.
Asali: UGC

"A tsige Sanusi II" - Mutanen Nasarawa

A Nasarawa, masu zanga-zangar sun yi kira da a tsige Sanusi II tare da mayar da Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano, in ji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun mamaye titin da ke kusa da gidan Aminu Ado Bayero na Nasarawa, inda ya yi zaman fadarsa bayan dawowarsa jihar.

Suna dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban, suna rera wakoki yayin da suke zagayawa kan tituna domin bayyanawa gwamnatin jihar bukatunsu.

Mutanen Gaya na adawa da rusa masarautu

Tun da fari, mun ruwaito cewa mazauna garin Gaya sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da rusa masarautar Gaya da gwamnatin jihar ta yi.

Masarautar Gaya na daga cikin masarautun da gwamnatin jihar Kano ta rusa bayan da aka yi wa dokar majalisar masarautun jihar ta 2019 kwaskwarima.

Kara karanta wannan

Rikicin sarautar Kano: Ɗan Sarki Sanusi II, Ashraf ya yi shaguɓe ga Aminu Ado Bayero

Masu zanga-zangar sun zargi gwamnati da rusa masarautun jihar saboda wasu dalilai na siyasa inda suka nemi gwamnan jihar da ya bi umarnin kotun tarayya.

Ka bi matakan doka - Sheikh Dahiru ga Abba

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi ya aika muhimmin sako ga masu ruwa da tsaki a rikicin masarautar Kano.

Sheikh Dahiru Bauchi ya nemi gwamnatin jihar da ta bi umarnin kotu na dakatar da aiwatar da dokar da ta rusa masarautu biyar na jihar domin wanzar da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel