Yan Bindiga Sun Hallaka Dalibai 2 da Suka Sace a Jami'a, Ƴan Sanda Sun Magantu

Yan Bindiga Sun Hallaka Dalibai 2 da Suka Sace a Jami'a, Ƴan Sanda Sun Magantu

  • Dalibai biyu daga cikin wadanda aka sace a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Osara a Kogi sun rasa ransu
  • Rundunar ƴan sanda a jihar ita ta tabbatar da mutuwar daliban inda ta ce miyagun sun yi ajalinsu a yau Lahadi
  • Kwamishinan yan sanda a jihar, Bethrand Onuoha shi ya tabbatar da haka a yau Lahadi 26 ga watan Mayu a cikin wata sanarwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Rundunar ƴan sanda a jihar Kogi ta sanar da mutuwar wasu daliban Jami'a da aka yi garkuwa da su.

Rundunar ta tabbatar da haka ne a yau Lahadi 26 ga watan Mayu ta bakin kwamishinan ƴan sanda, Bethrand Onuoha a birnin Lokaja.

Kara karanta wannan

Ana cikin ɗimuwa bayan jirgi daga Kaduna zuwa Abuja ya carke a daji, sojoji sun ja daga

Yan bindiga sun yi ajalin daliban Jami'a da suka sace
Yan bindiga sun hallaka wasu daliban Jami'a 2 da suka sace a farkon wata. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun hallaka daliban Jami'a 2

Daliban guda 2 sun gamu da ajalinsu ne bayan sace su daga Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta (CUSTECH) da ke Osara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bethrand ya ce kisan daliban abin takaici ne da kuma Allah wadai, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai Kwamishina bai yi karin haske kan lamarin ba amma ya tabbatar da cewa rundunar ta bazama neman maharan domin daukar mataki, cewar Vanguard.

Yan bindigan sun farmaki Jami'ar a ranar 9 ga watan Mayu da misalin karfe 9:00 na dare lokacin da dalibai ke tsaka da karatun jarrabawa.

Yadda yan bindiga suka sace daliban Jami'a

Miyagun sun yi ta harbi sama inda suka rikita daliban kafin suka kutsa kai ciki tare da sace dalibai da dama.

Daga bisani jami'an tsaro sun yi nasarar ceto ɗalibai 21 daga cikinsu da taimakon yan farauta da ke yankin.

Kara karanta wannan

Rundunar sojojin Najeriya ta fatattaki 'yan ta'adda, an kamo miyagu a Abuja da Oyo

Duk da haka akwai sauran daliban da ke hannun yan bindigan kafin kisan guda biyu daga cikinsu.

An kama dan Kamaru da garkuwa da mutane

A wani labarin, Jami'an tsaron farin kaya da ƴan sandan jihar Delta sun kama wani mutumin kasar Kamaru bisa zargin garkuwa da mutane.

Ana zargin mutumin ya yi haɗaka da wasu 'yan Najeriya su biyu wajen gudanar da ayyukan ta'addanci a jihar Delta.

Ana zarginsu da yin garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta'addanci a yankunan Orerokpe, Sapele da Warri a jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel