Gwamnatin Tinubu Ta Fusata da Dabi’un Gwamnonin Najeriya, Ta Maka Su a Kotun Koli

Gwamnatin Tinubu Ta Fusata da Dabi’un Gwamnonin Najeriya, Ta Maka Su a Kotun Koli

  • Gwamnatin tarayya ta maka gwamnonin 36 a gaban Kotun Koli domin tabbatar da cin gashin kan kananan hukumomin kasar
  • Babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a (AGF) ne ya shigar da karar karar mai lamba SC/CV/343/2024 a ranar 20 ga Mayu
  • Gwamnatin tarayyar na rokon kotun da ta ba da umarnin a rika tura kudin kananan hukumomi kai tsaye zuwa asusun su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja – Gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta maka gwamnonin jihohin tarayya 36 zuwa Kotun Koli.

Gwamnatin tarayya ta dauki mataki kan gwamnoni 36 na Najeriya
Gwamnatin ttarayya ta yi karar gwamnonin Najeriya 36 a Kotun Koli. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Matakin da aka dauka na shari’a kan gwamnoni 36 ya biyo bayan rashin da’a da ake zarginsu da aikatawa a harkokin gudanar da kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Abincin wasu ya kare: Gwamna ya kori shugabannin kananan hukumomi 16 a jiharsa

Gwamnati ta maka gwamnoni a kotu

Babban lauyan tarayya kuma ministan shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ya shigar da karar mai lamba: SC/CV/343/2024, in ji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Prince Fagbemi ta hanyar gwamnatin tarayya yana neman cikakken 'yancin cin gashin kai ga dukkanin kananan hukumomin kasar nan.

Gwamnatin tarayya na rokon Kotun Kolin da ta bayar da umarnin haramta wa gwamnonin jihohi rusa shugabannin kananan hukumomi da aka zaba ba bisa ka’ida ba.

Bukatun gwamnati ga Kotun Koli

Jaridar The Nation ta ruwaito gwamnatin tarayyar na rokon kotun da ta ba da umarnin a rika tura kudin kananan hukumomi kai tsaye zuwa asusun su daga na tarayya.

Wannan matakin yana daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulki wanda ya sabawa asusun hadin gwiwa da gwamnoni suka yi ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga mayar da Sanusi II gidan sarauta

Gwamnatin tarayyar na kuma son kotun ta ba da umarnin hana gwamnoni kafa kwamitocin rikon kwarya don tafiyar da al’amuran kananan hukumomi sabanin yadda tsarin mulkin kasar ya amince

Gwamna ya rantsar da kwamishinoni 8

A wani labarin, mun ruwaito gwamnan jihar Rivers, Siminilayi Fubara ya rantsar da sababbin kwamishinoni takwas da majalisar jihar ta tantance a baya.

Wannan na zuwa ne bayan da wasu kwamishinonin jihar guda hudu suka yi murabus daga mukaminsu a gwamnatin Fubara kan rikicikin siyasa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel