Sarkin Kano: Zanga Zanga Ta Barke a Fadar Masarautar Gaya da Majalisa Ta Rusa

Sarkin Kano: Zanga Zanga Ta Barke a Fadar Masarautar Gaya da Majalisa Ta Rusa

  • Kwanaki kadan da tsige sarakuna biyar na masarautun Kano, zanga-zanga ta barke a karamar hukumar Gaya domin nuna adawa ga gwamnati
  • Masu zanga-zangar sun nuna bakin cikin su kan rusa masarautun suna masu yin zargin cewa matakin na da alaka da siyasa ne kawai
  • Idan ba a manta ba, gwamnan Kano, Abba Yusuf ya ce ya mayar da Muhammadu Sanusi kan karagar Sarkin Kano saboda cika alkawari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gaya, jihar Kano - anzu haka dai zanga-zanga ta barke a titunan Gaya daya daga cikin masarautu biyar da sabuwar dokar majalisar Masarautar Kano ta shafa.

Zanga-zanga ta barke a Gaya, jihar Kano
Sakamakon rusa masarautun Kano, zanga-zanga ta barke a karamar hukumar Gaya. Hoto: @ImamShams, @muhsintasiuyau
Asali: Twitter

Mutane na adawa da rusa masarautu

Mazauna garin sun shaida wa manema labarai cewa, Sarkin da aka tsige na Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya bar fadar ne da tsakar daren ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Sarki 2 a lokaci 1: Lauyoyin Kano sun fitar da jawabi ganin an jibge jami'an Sojoji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu wata alamar tashin hankali ko turjiya a yayin gudanar da zanga-zangar domin akwai jami'an tsaro a ko ta ina, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin garin Abubakar Shuaibu ya ce mutane da dama a Gaya ba su ji dadin wannan mataki da gwamnatin jihar ta dauka ba.

Zanga-zanga ta barke a titunan Gaya

A safiyar Lahadin nan, wani faifan bidiyo da wani Kawu Garba ya wallafa a shafinsa na X ya nuna yadda mazauna garin suka yi dafifi kan tituna domin kin amincewa da rusa masarautar.

Masu zanga-zangar dai suna dauke da manyan kwalaye da kuma rera wakokin nuna adawa da gwamnati, suna mai yin zargin cewa rusa masarautan na da alaka da siyasa.

Kalli bidiyon a nan kasa:

Majalisar dokokin Kano ta soke dokar da tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi amfani da ita wajen tsige Alhaji Muhammadu Sanusi II a shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Sabon sarki: Matasa sun yi a zanga zanga, sun nemi Tinubu ya takawa Abba birki

Dalilin mayar da Sanusi II Sarkin Kano

Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya bayyana dalilin da ya sa ya mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano.

Gwamna Abba ya bayyana cewa mayar da Sanusi II gidan sarauta cika alkawari ne da ya daukarwa mutanen Kano tun a lokacin yakin neman zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.