Minista Ya Maidawa Tsohon Ministan PDP Raddi a Twitter Kan Rikici da Kasar UAE

Minista Ya Maidawa Tsohon Ministan PDP Raddi a Twitter Kan Rikici da Kasar UAE

  • Osita Chidoka ya soki mahukuntan Najeriya a kan maido alaka da kamfanin jiragen sama na Emirates da aka yi
  • Shi kuma Festus Keyamo SAN ya gagara kauda idanunsa, ya dauki lokaci ya maida martani a shafinsa na X (Twitter)
  • Ministan jiragen saman yana ganin kishin karya Chidoka yake nunawa, a karshe ya caccaki har da Alhaji Atiku Abubakar

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Osita Chidoka wanda ya yi ministan harkokin jiragen sama a Najeriya, ya yi magana a kan dambarwar kamfanin jirgin saman Emirates.

Osita Chidoka ya nuna babu wani abin farin ciki saboda kamfanin Emirates sun dawo aiki da Najeriya bayan sun dakatar da yin hulda a baya.

Minista
Minista ya kare matakin dawo da kamfanin jirgin Emirates daga UAE Hoto: @FKeyamo
Asali: Twitter

Ministan jirage ya maidawa Chidoka martani

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Lauya ya lalubo lungun da Abba ya saba doka wajen maido Sanusi II

Kamar yadda ya yi magana a shafinsa na X a baya, Chidoka ya nuna an sa kwadayi a maimakon kishin kasar da aka san Najeriya da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Ministan yana da ra’ayin cewa bai dace a lallabo kamfanin Emirates ba duba da yadda suka yi watsi da Najeriya da aka shiga matsi.

Amma Festus Keyamo SAN wanda shi ne ministan harkokin jiragen sama a yau, ya yi watsi da wannan ra’ayi da magabacin nasa yake da shi.

Festus Keyamo ya ce idan dai da gaske Chidoka yana da kishin-kasa, kamata ya yi ya ba Atiku Abubakar shawarar saida kadarorinsa a Dubai.

Minista ya hada da Atiku Abubakar

A lokacin da jiragen Emirates suka daina aiki har ta kai an hana ‘yan Najeriya bizar Dubai, Keyamo ya ce ya kamata Atiku ya nuna kishinsa.

Kara karanta wannan

Manyan malamai sun fayyace hukuncin Crypto da ‘Mining’ a addinin Musulunci

Ministan yana ganin jagoran na jam’iyyar PDP karyar kishin kasa yake yi idan aka yi la’akari da kusancin Atiku Abubakar da kasar UAE.

A ra’ayin Lauyan, babu dalilin rigima da mahukuntan UAE lura da yadda ‘yan Najeriya irinsu Allen Onyema suka narka kudinsu a kasar.

Kiran Keyamo zuwa ga tsohon Minista

"Maimakon karyar nuna kishin kasa, kyau ka yiwa mutanen Najeriya bayanin matsalar tattalin arzikin da za a iya samu a dalilin haka, idan har akwai.
Ina ba jam’iyyar PDP ta ku shawarar dagewa sosai wajen sake karbar mulki a 2027 watakila sai ku cigaba da fada da hukumomin UAE bayan nan."

Zargin ashawa a gwamnatin Najeriya

Kwanaki an samu labari cewa ana zargin an rika karbar dalolin cin hanci a lokacin da Godwin Emefiele yake rike da bankin CBN.

Wani ‘dan kwangila, Victor Onyejiuwa ya ce shugabannin CBN sun sa ya biya cin hancin kusan Naira miliyan 300 kafin a sallame shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng