Yan Sanda Sun Yi Biyayya Ga Kotu, 'Har Yanzu Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano'

Yan Sanda Sun Yi Biyayya Ga Kotu, 'Har Yanzu Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano'

  • A safiyar yau ne Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya iso Kano da rakiyar jami'an tsaro da ake zargin ofishin mai ba wa shugaban kasa shawara ne ya bayar da su
  • Sai dai gwamnatin Kano ta umarci kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Muhammed Usaini Gumel da ya gaggauta kamo tsohon sarkin da a yanzu ke fadar sarki ta Nassarawa
  • Amma a taron manema labarai da ya gudanar a yau, CP Muhammed Usaini Gumel ya bayyana cewa har sun bi umarnin kotu da ke cewa har yanzu Aminu Ado Bayero ne sarki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano-Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Muhammed Usaini Gumel ya bayyana cewa har yanzu suna bin umarnin kotu da ta hana gwamnatin Kano nada sabon sarki.

Kara karanta wannan

Kano: Lamura sun dagule bayan matasa dauke da makamai sun cika fadar Sarki, bayanai sun fito

Ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar 'yan sandan a safiyar yau bayan rahoton dawowar Alhaji Aminu Ado Bayero Kano.

Yan sanda
Yan sanda a Kano sun yi biyayya ga umarnin Kotu, Aminu Ado Bayero ne Sarki
Asali: Facebook

A taron da DCL hausa ta dauka kai tsaye ta shafinta na facebook, kwamishinan ya yi bayanin cewa suna biyayya ga umarnin kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ya jaddada cewa an shirye suke su tabbatar da tsaron rayukan al'umar Kano da dukiyoyinsu duba da halin da jihar ke ciki.

'Kotu ta haramta nada sabon sarki,' Gumel

Kwamishinan 'yan sandan ya bayyana cewa ba za su yi biyayya ga wani umarni da ya wuce na kotu ba, bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci a kamo tsohon sarki, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Ya bayyana cewa a umarnin kotu, dole a dakata da nada sabon sarki har sai ta fara sauraren shari'a kan batun ranar 3 ga watan gobe.

Kara karanta wannan

Kano: Sojoji sun ja daga yayin da Abba Kabir ya umarci cafke Aminu Ado Bayero

Wannan na nufin har yanzu Aminu Ado Bayero ne sarkin kano maimakon Malam Muhammadu Sunusi na II da gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada.

Ya gargadi masu kokarin tada zaune tsaye da cewa a shirye suke su dakile yunkurin hakan.

Sojoji sun kawowa Sarki Aminu kariya

A baya mun kawo muku rahoton cewa an sake turo sojoji daga babban birnin tarayya Abuja domin bawa sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero kariya.

Wannan na zuwa bayan umarnin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar na a kama tsohon sarkin saboda kokarin tayar da tarzoma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel