"Zan Yi Bincike," Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Mayar da Sarki Sanusi II Kan Mulki
- Rabiu Kwankwaso ya ce zai nemi karin bayani kan yadda aka sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano idan ya koma gida
- Tsohon gwamnan yana Abuja lokacin da aka naɗa sarkin amma ya ce ba bu hannunsa a dawo da Sarki Sanusi
- Jagoran Kwankwasiyya shi ne ake ganin yana da ƙarfin faɗa-a-ji a gwamnatin Abba Kabir Yusuf kuma dama ya taba magana kan lamarin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Jagoran NNPP na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce bai sa baki a mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan karaga ba.
Idan baku manta ba Kwankwaso ya fara naɗa Sanusi a matsayin sarkin Kano a 2014, amma Abdullahi Ganduje, wanda gaje shi ya tuɓe sarkin a 2020.
To sai dai tun bayan nasarar jam'iyyar NNPP a zaɓen gwamnan jihar Kano a 2023, Kwankwaso ya ce za su duba yadda aka sauke Sanusi daga sarauta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jiya Alhamis, majalisar dokokin jihar Kano ta canza dokar masarautar Kano wanda ya bai wa Sanusi ƙofar komawa kan karagar mulki, cewar Daily Trust.
Kwankwaso zai binciki naɗin Sanusi
Da yake zantawa da BBC Hausa kan batun, Kwankwaso ya ce nan kusa zai koma Kano kuma zai gano yadda aka yi aka mayar da Khalifan Tijjaniya kan mulki.
Ya ce:
"Kwankwaso ya ƙona hannunaa kan ya ce ga yadda za a yi, shi gwamna muna tare da shi muna aiki tare, saboda kullum mu abin da muke shi ne idan an tambaye ni zan ba da shawara idan ba a tambaye ni ba shikenan."
"Su je yi abin da suka ga ya dace kuma mu zamu masu kyakkyawar addu'a Alla ya ci gaba da taimakonsu."
Kwankwaso ya sa aka naɗa Sanusi II?
Yayin da aka nemi yayi ƙarin haske kan abin da yake nufi da za su sake duba yadda Ganduje ya sauke Sanusi, Kwankwaso ya ce ko a lokacin bai faɗi ga yadda za a yi ba.
"Ai da nace za a duba ai bance za ayi hagu ko dama ba, kuma ga shi sun duba, idan na koma zan ji meya faru kuma ya aka yi na tabbata za su yi mini cikakken bayani.
"Kuma duk abin da suka faɗa shikenan sai mu masu addu'a. Mu dama abin da muka ce su je su duba su gani shin an yi abin nan bisa son zuciya ko tsakani da Allah?"
- cewar Kwankwaso.
Da muka zanta da wani mamban NNPP kuma ɗan Kwankwasiyya ya ce su fa matakin da Abba ya ɗauka ya masu daidao domin sun jima suna dakon wannan rana.
Malam Sai'du, mazaunin Hotoro a Kano ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa hanyar da tsohon gwamna ya bi ya tarwatsa masarautar Kano, ita aka bi aka dawo da ita.
A kalamansa ya ce:
"Ba zan ɓoye maka ba mutanen Kano sun rabu biyu, akwai masu jin daɗin dawo da Sanusi akwai kuma waɗanda ke ganin bai kamata ba. Ku cire zancen mai gida Kwankwaso, mu dama haka muke so.
"Abba ya yi kamfe da lamarin masarautun nan, don haka ko jagora ya tuna masa dai alƙawari ne da ya ɗauka kuma ya cika, Allah ya ƙara wa Sarki Sanusi lafiya."
Muhammadu Sanusi ya koma kan mulki
A wani rahoton kuma kun ji cewa Muhammadu Sanusi II ya koma kan kujerar Sarkin Kano karo na biyu a hukumance yau Jumu'a, 24 ga watan Mayu, 2024.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa Sanusi takardar shaidar naɗa shi sarkin Kano a wani taro da aka shirya a gidan gwamnatin Kano.
Asali: Legit.ng