"Ina Godiya Abba": Sarki Sanusi II Ya Magantu Bayan Dawowa Kujerarsa

"Ina Godiya Abba": Sarki Sanusi II Ya Magantu Bayan Dawowa Kujerarsa

  • Sabon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusufu da ƴan majalisar dokoki kan mataki da suka ɗauka
  • Muhammadu Sanusi II ya ce tabbas duk abin da Allah SWT ya ƙaddara, babu wanda ya isa hana shi afkuwa tun da tun farko Ya tsara abinsa
  • Sarkin ya bayyana haka ne a yau Juma'a 24 ga watan Mayu jim kadan bayan karbar takardar mayar da shi kan kujerar sarauta a gidan gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarki Muhammadu Sanusi II ya magantu bayan mayar da shi kan kujerar sarautar jihar Kano.

Mai Martaba ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf da majalisar jihar kan nuna jarumta wajen daukar wannan mataki.

Kara karanta wannan

Sabon sarki: Matasa sun yi a zanga zanga, sun nemi Tinubu ya takawa Abba birki

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yabawa Abba Kabir
Sarki Muhammadu Sanusi II ya godewa Abba Kabir na Kano. Hoto: @Babarh.
Asali: Twitter

Kano: Sanusi II ya godewa Abba Kabir

Sanusi II ya ce hakan ya nuna cewa idan Allah ya kaddari abu babu wanda ya isa ya hana faruwar hakan, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon Sarkin ya bayyana haka ne jim kadan bayan karbar takardar mayar da shi sarautar jihar a gidan gwamnati a yau Juma'a 24 ga watan Mayu.

Ya ce haka Allah ya tsara kuma babu wanda zai iya sauya hukuncinsa kan sarautar jihar.

Sarki Sanusi II ya ce tsarin Allah ne

"Larabawa suna cewa duk abin da zamu fuskanta akwai darasi a ciki da ke nuna cewa akwai Allah."
"Duk abin da zai faru da dan Adam, Allah ya tsara shi kuma hakan darasi ne ga masu hankali."
"Allah daya ne, kuma duk abin da zai yi babu mai hanawa, abin da kuma yaki yi babu wanda ya isa yasa haka ya faru."

Kara karanta wannan

Sarki Muhammadu Sunusi II ya jagoranci sallarJuma'a a fadar Gwamnatin Kano

- Muhammadu Sanusi II

Sanusi II ya jagoranci sallar Juma'a a Kano

A wani labarin, kun ji cewa, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya jagoranci sallar Juma'a a masallacin dake fadar gwamnatin Kano.

Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana cewa sabon sarkin ne zai jagorance su sallah jim kadan bayan tabbatar da shi a matsayin sabon sarkin Kano.

Hakan ya biyo bayan mayar da Sarkin kan sarautar jihar a yau Juma'a 24 ga watan Mayu a gidan gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.