Sojojin Najeriya sun Fatattaki 'Yan Ta'adda, an Kamo Miyagu a Abuja da Oyo

Sojojin Najeriya sun Fatattaki 'Yan Ta'adda, an Kamo Miyagu a Abuja da Oyo

  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun farmaki wata maboyar masu garkuwa da mutane a babban birnin tarayya Abuja, inda suka kama mutane uku ciki har da mata
  • Ana zargin matasa Raham Abubakar, Sadiya Mohammed da Ashiru Muhammed da laifin ba wa ma su garkuwa da mutane mafaka da taimaka masu da bayanan sirri
  • Haka ma a jihar Oyo an kama wani Usman Mohammed Aliyu da kudi N400,000, ya amsa cewa ya dade a mummunan aikin satar mutane da shanun jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Rundunar sojojin Najeriya ta samu galaba kan wasu masu garkuwa da mutane dake cin kasuwarsu a Abuja da jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Sabon sarki: Matasa sun yi a zanga zanga, sun nemi Tinubu ya takawa Abba birki

A wani samame da jami'an sojojin suka kai maboyar 'yan ta'addan a Ajegunle Mpape dake Abuja, sun koro bata-garin tare da cafke mutane uku.

Rundunar sojoji
Sojoji sun yi galaba kan 'yan ta'adda Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

A jawabin da rundunar ta wallafa a shafinta na X, an kai samamen ne bayan samun bayanan sirri na ayyukan 'yan ta'adda yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama masu ba bata-gari bayanai

Rundunar sojojin kasar nan ta kama wasu mutane uku a karamar hukumar Bwari dake Abuja bisa zargin tattaro bayanai, suna mikawa masu garkuwa da mutane.

Leadership News ta tattaro cewa an kama Ashiru Muhammed da wasu mata guda biyu; Raham A bubakar da Sadiya Mohammed a samamen.

Abubuwan da sojojin suka kwace

Sojojin sun samu nasarar gano bindiga kirar Pistol da alburusai 21 da katin cirar kudi (ATM) na bankuna biyar daga maboyar bata-garin.

Sauran abubuwan da aka kwace sun hada da miyagun kwayoyi da wayoyin hannu guda biyu, kuma an tattare su duka zuwa rundunar.

Kara karanta wannan

Filato: Adadin mutanen Zurak da suka mutu a harin 'yan bindiga ya karu

An kama mai satar mutane a Oyo

Wani Usman Mohammed Aliyu ya shiga komar sojoji a yankin Igboho-Igbeti dake jihar Oyo lokacin da ake bincike a kan hanyar bayan samun rahoton sirri kan zirga-zirgar bata-gari a yankin.

An kama shi da kudi ₦400,000, kuma ya amsa laifin satar shanu da mutane a yankunan. Rundunar sojojin ta ce ana zurfafa bincike kafin daukar matakin da ya dace.

DHQ ta fusata kan zargin ta'addanci

A baya mun kawo muku labarin cewa hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta kalubalanci Gwamnatin jihar Katsina kan zargin wasu daga jami'anta na hada baki da 'yan ta'adda.

DHQ ta mayarwa gwamna Dikko Radda raddi, inda ta ce dukkanin jami'anta na biyayya ga kundin tsarin mulkin kasa, kuma ta 'yan Najeriya ce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.