Dattawan Arewa Sun Yi Magana Kan Sake Naɗa Sanusi II a Matsayin Sarkin Kano
- Dattawan Arewa sun nuna damuwa kan yadda ake ƙara samun yawaitar sauya sarakuna a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma
- Kungiyar dattawan NEF ta buƙaci gwamnatin Kano da waɗanda abin ya shafa su tafiyar da batun dawo da Sanusi II cikin kulawa da kwarewa
- NEF ta kuma yi kira ga mutane su kwantar da hankulansu, kar su yarda su tada zaune tsaye kan abin da ke faruwa a jihar Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta nuna matuƙar damuwa kan abubuwan da ke faruwa a jihar Kano, inda ake ta sauye-sauyen sarakuna a ƴan shekarun nan.
NEF ta bayyana cewa abin da ke faruwa a Kano babbar alama ce da ke nuna yadda sarakuna ke fuskantar ƙalubale a ƙasar nan.
Har ila yau NEF ta nuna damuwa kan sauya Sarkin Kano da aka yi wanda ya haifar da fargaba a tsakanin mutane da ƴan Najeriya masu kishin ƙasa, rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta kuma bukaci gwamnatin jihar Kano da ‘yan siyasa da abin ya shafa da su yi taka-tsan-tsan wajen tunkarar wannan batu mai muhimmanci domin hana tada zaune tsaye.
Idan ba ku manta ba a jiya Alhamis, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano bayan rushe masarautu 5.
Gwamna Abba ya dawo da Sarkin Kano na 14 ne bayan majalisar dokoki ta sabunta dokar masarautu tare da tsige dukkan sarakuna biyar da Ganduje ya naɗa, cewar Premium Times.
NEF ta yi magana bayan naɗa Sanusi II
Da take mayar da martani kan haka, kungiyar datttawan Arewa (NEF) ta ce ya kamata dukkan bangarorin da abin ya shafa su tunkari lamarin cikin matukar kulawa da kwarewa.
Mai magana da yawun NEF, Abdul-Azeez Suleiman ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu.
"Ɗaukar matakin gaggawa da kalaman tunzura kan iya dagula al'amura kuma su kawo cikas ga zaman lafiya a jihar Kano," in ji NEF.
NEF ta buƙaci a zauna lafiya a Kano
Dattawan Arewa sun yi kira ga al'umma musamnan mazauna Kano su kwantar da hankulansu kana su zama masu bin doka da oda.
Sun jaddada cewa yana da matukar muhimmanci kar mutane su yi duk wani abu da zai iya kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.
Sarki Sanusi ya shiga gidan gwamnatin Kano
Rahotanni sun nuna cewa Sarki Muhammadu Sanusi ya isa gidan gwamnatin jihar Kano da safiyar ranar Jumu'a, 24 ga watan Mayu, 2024.
Sarkin zai karɓi takadar mayar da shi kan kujerar sarautar Kano daga hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf sannan ya wuce fadar Nasarawa.
Asali: Legit.ng