Ba zai Yiwu ba," Gwamnati ta Mayarwa NLC Martani kan Mafi Karancin Albashi

Ba zai Yiwu ba," Gwamnati ta Mayarwa NLC Martani kan Mafi Karancin Albashi

  • Yayin da kungiyar kwadago ta rage buri tare da sake tayin sabon mafi karancin albashi ga gwamnati, har yanzu ana ganin N497,000 a matsayin mafi karancin albashi ya yi yawa
  • Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Akwa Ibom Effiong Essien ya bayyana cewa kudin da NLC ta nema ba zai yiwu ba, domin gwamnati ta yi tayin biyan N57,000 ga kungiyoyin
  • Ya na ganin kamata ya yi NLC ta fitar da sabon mafi karancin albashin da gwamnatocin jihohi za su iya biya, domin a shirye suke a cimma matsaya domin samun mafita

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Akwai Ibom- Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta shawarci gamayyar kungiyoyin kwadago su daina mafarki.

Kara karanta wannan

Gwamna Lawal ya kafa tarihi, ma'aikata za su sha romon mafi ƙarancin albashi bayan shekaru

Kungiyar Kwadago ta NLC dai na neman gwamnatin tarayya ta amince da N497,000 a matsayin mafi karancin albashi ma'aikata.

Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta shawarci gamayyar kungiyoyin kwadago su daina mafarki.

Kwadago
Gwamnati ta ce ba za ta iya biyan N497,000 a matsayin mafi karancin albashi ba Hoto: @NLCHeadquaters
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa gwamnatin tarayya ta yi tayin N57,000, lamarin da kungiyar kwadagon ke ganin rainin wayo ne. Da farko gwamnatin ta ce za ta biya N48,000 amma kungiyoyin kwadago suka yi fatali da tayin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Albashin nawa gwamnati za ta iya biya?

Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Akwa Ibom, Effiong Essien, ya ce a shirye gwamnati ta ke wajen cimma matsaya. Amma ya bayyana cewa dole ne NLC ta bijiro da abin da hankali zai dauka, kamar yadda Daily Post ta wallafa.

Shugaban na ganin gwamnatocin jihohi ba za su iya biyan abin da NLC ke bukata ba.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: NLC ta sauko daga bukatar N615,000, ta fadi sabon tayi

Effiong Essien, ya kuma bayar da shawarar rage daukar ma'aikata masu yawa lokaci guda, domin lokacin ritayarsu kan zo daya. Ya ce ritaya lokaci guda kuma na kawo cikas na karancin ma'aikata a lokacin da ake bukatarsu.

NLC ta fusata da karin kudin wuta

A baya mun ruwaito muku cewa kungiyar kwadago ta NLC ta murza gashin baki inda ta ba gwamnatin tarayya wa'adi kan karin kudin wuta da aka yi.

Kungiyoyin kwadago ta NLC da ta 'yan kasuwa ta TUC sun ce ba za su lamunci karin kudin ba, aka ba gwamnatin zuwa karshen Mayu ta janye karin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel