Sarkin Kano: Duk da Umarnin Kotu, Gwamna Abba Zai Mika Takardar Nadi Ga Sanusi II
- Gwamna Abba Kabir Yusuf zai gabatar da takardar nadi ga mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II na 16
- Za a gudanar da taron mika takardar nadin ne da misalin karfe 9:00 na safiyar yau Juma'a a dakin taro na fadar gwamnati
- Wannan kuwa na zuwa ne bayan da babbar kotun tarayya da ke jihar ta umarci gwamnatin jihar da ta dakatar da nada Sanusi II
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta bayyana lokacin da za ta ba Muhammadu Sanusi II takardar nada shi sarautar Sarkin Kano na 16.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne zai gabatar da takardar nadin ga Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 16 a Africa House dake fadar gwamnatin Kano.
Mai taimakawa gwamnan Kano na musamman kan kafofin sadarwa na zamani, Abdullahi I. Ibrahim ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta hana nada sabon Sarkin Kano
Wannan kuwa na zuwa ne bayan da wata babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ta umarci gwamnatin jihar da ta dakatar da nada Sanusi II.
Mun ruwaito Mai shari’a Mohammed Liman ya bayar da wannan umarni ne a cikin karar da Sarkin Dawaki Babba na masarautar Kano, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar.
Alkalin kotun ya kuma umarci gwamnatin jihar da ta dakatar da aiwatar da dokar da majalisar dokokin Kano ta yi na rusa masarautu biyar na jihar.
Gwamna Abba zai ba Sanusi II takarda
Sai dai a wannan sanarwa da Abdullahi I. Ibrahim ya fitar a safiyar Juma'a, ya ce Gwamna Abba zai ba Sanusi II takardar nadin ne da karfe 9:00 na safiyar yau.
Mai taimakawa gwamnan ya ce:
"Da misalin karfe 9:00 na safiyar yau Gwamna Abba Kabir Yusuf zai gabatar da takardar nadi ga mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a Africa House dake fadar gwamnatin Kano."
"Dalilin nada Sanusi II Sarkin Kano" - Abba
Tun da fari, mun ruwaito Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na daya daga cikin alkawuran da ya daukarwa mutanen Kano.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar da sanarwa kan hakan, inda ya ce gwamnan ya ba sarakunan da aka tsige wa'adin awanni 48 su bar gidajen sarauta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng