Gwamna Abba Ya Sa Labule da 'Yan Majalisa, Masu Nada Sarki a Kano, Bayanai Sun Fito
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanya labule da ƴan majalisar dokokin jihar da masu naɗa sabon Sarki
- Ganawar gwamnan da mutanen na zuwa ne bayan majalisar dokokin jihar ta amince da sabon ƙudirin dokar da ya yi wa dokar kafa masarautun jihar garambawul
- Ana sa ran Gwamna Abba zai rattaɓa hannu a dokar wacce ta rushe sababbin masarautun da aka ƙirƙiro a lokacin mulkin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shiga ganawar sirri da ƴan majalisar dokokin jihar a gidan gwamnatin jihar.
A ganawar da gwamnan ya shiga har da wasu masu riƙe da sarautun gargajiya da ake kyautata zaton masu naɗa Sarki ne.
Ana sa ran gwamnan zai sanya hannu kan ƙudirin dokar da majalisar dokokin jihar ta amince da shi tun farko a ranar Alhamis wanda ya rushe sababbin masarautu da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhammad Sanusi II zai zama sabon Sarki
Idan Gwamna Abba ya sanya hannu kan wannan ƙudirin dokar, ana sa ran za a dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, wanda aka tsige a watan Maris ɗin 2020, cewar rahoton tashar Channels tv.
Sai dai har yanzu ba a san makomar Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ba.
Rahotanni sun ce Sarki Aminu Ado Bayero ba ya Kano a halin yanzu bayan da ya ziyarci Oba Sikiru Adetona, Awujale na Ijebuland, a ranar Laraba.
Gwamnatin Rabiu Kwankwaso ta nada Muhammad Sanusi II, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), a matsayin Sarkin Kano na 14 a watan Yunin 2014.
Gwamna Abba ya rushe masarautun Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sanya hannu kan dokar da ta rusa masarautun jihar.
Gwamnan ya sanya hannun ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu bayan mika masa takarda mai ɗauke da dokar a gidan gwamnatin jihar.
Rattaba hannu kan dokar ya sake tabbatar da rushe masarautun guda biyar da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng