Ta Faru Ta Kare: Masu Nadi Sun Isa Gidan Gwamnati, Zasu Fara Nadin Sabon Sarkin Kano

Ta Faru Ta Kare: Masu Nadi Sun Isa Gidan Gwamnati, Zasu Fara Nadin Sabon Sarkin Kano

  • A yanzu haka masu nadin sabon Sarki sun samu shiga gidan gwamnatin Kano domin daukar mataki kan kujerar sarautar jihar
  • Masu nadin saraurar sun shiga gidan gwamnatin ne domin fara shirye-shiryen nada sabon Sarkin Kano ba tare da bata lokaci ba
  • Hakan ya biyo bayan rusa masarautun jihar guda biyar da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro a watan Disambar shekarar 2019

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Masu nadin sabon Sarki sun isa gidan gwamnatin jihar Kano domin fara shirye-shirye.

Hakan ya biyo bayan rusa masarautun jihar guda biyar da Majalisar dokokin jihar ta yi a yau Alhamis 23 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Abba ya tabbatar da korar Aminu Ado Bayero, ya sanya hannu a dokar da ta rusa su

An fara shirye-shiryen nada sabon Sarkin Kano
Masu nadin sarauta sun isa gidan gwamnati domin nada sabon Sarkin Kano. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Masarautar Bichi.
Asali: Facebook

Wadanda suka je nada sabon Sarkin Kano

Daga cikinsu akwai Madakin Kano da hakimin Dawakin-Tofa da Yusuf Nabahani da Makaman Kano, cewar Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da Hakimin Wudil da Abdullahi Sarki-Ibrahim da Sarkin Dawaki Mai Tuta da sauransu.

Wata majiya ta tabbatar da cewa masu nadin sarautar sun kammala ganawa da Gwamna Abba Kabir kan lamarin, Daily Trust ta tattaro.

Majiyar ta ce bayan ganawar sun yanke shawarar dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon sarkin Kano.

Majalisar Kano ta fadi makomar sarakuna 5

Kamar yadda majalisar ta tabbatar ta bakin shugaban masu rinjaye, Hussaini Lawal Chediyar Yan Gurasa ta fada, a yanzu dukkan sarakunan sun bar kujeraunsu.

Lawal ya ce ya rage gwamnan ya zabi Sarkin sa ya ke so domin ci gaba da jagorantar sarautar jihar.

Kara karanta wannan

Dawo-Dawo: An sanar da sabon Sarkin Kano, Sanusi II ya zama sarki a karo na biyu

Hakan ya biyo bayan ƙirƙirar masarautun da Abdullahi Ganduje ya yi a ranar 5 ga watan Disambar 2019 inda aka tumbuke Muhammadu Sanusi II a shekarar 2020.

Fubara ya taya Sarki Sanusi II murna

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya taya Mai Martaba, Muhammadu Sanusi II murnan dawowa kujerar sarautar Kano.

Fubara ya bayyana haka ne a yau Alhamis 23 ga watan Mayu yayin taron bunkasa tattalin arziki a jihar wanda Sanusi II ya halarta.

Gwamnan ya ce ya yi farin ciki da samun wannan labari inda ya yabawa Gwamna Abba Kabir kan wannan mataki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.