Kano: Gwamnan PDP Ya Taya Muhammadu Sanusi II Murna Game da Dawowa Karaga

Kano: Gwamnan PDP Ya Taya Muhammadu Sanusi II Murna Game da Dawowa Karaga

  • Yayin da ake ta yaɗa cewa za a mayar da Muhammad Sanusi II kan kujerarsa, Gwamna Simi Fubara na Rivers ya magantu
  • Mai girma Gwamna Fubara ya taya Mai Martaba Muhammadu Sanusi na II murnan sake dawowa kan sarautar jihar Kano
  • Wannan na zuwa ne bayan Majalisar jihar ta rusa dukkan masarautun da gwamnatin Ganduje ta kirkira guda biyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya taya Mai Martaba Muhammadu Sanusi II kan komawa kujerarsa.

Siminalayi Fubara ya ce ya ji dadin samun labarin kokarin mayar da Muhammadu Sanusi kujerarsa a matsayin Sarki na 14.

Gwamna Fubara ya taya Muhammadu Sanusi II murna
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya taya Muhammadu Sanusi II murnan dawowa kujerar sarautar Kano. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Fubara ya yi murnar dawowar Sanusi

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da Ganguje yake shaguɓe ga Muhammadu Sanusi II bayan tube shi

Wannan na zuwa ne yayin aka yada jita-jitar cewa za a mayar da Sanusi II kan kujerarsa, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce hakan ya sanya shi farin ciki ganin yadda Sanusi yake jihar domin taron masu zuba hannun jari.

Ya ce dawo da Sanusi ya nuna cewa cire shi a watan Maris din shekarar 2020 bai yi wa jama'ar jihar Kano dadi ba, The Nation ta tattaro.

Har ila yau, gwamnan ya yabawa Abba Kabir kan jin koken jama'ar jihar inda ya bukaci ƴan jihar su ba Sarkin dukkan goyon baya.

"Ina yiwa Sarkin Kano na 14 fatan alheri da yin mulki cikin nasara domin kawo ci gaba a jihar baki daya."

- Simi Fubara

Gwamna ya yabawa Abba da Sanusi II

Fubara ya bukaci shugaban na Tijjaniya da ya jagoranci fiye da mutane miliyan 50 da ke karkashinsa domin samun zaman lafiya a jihar da ma Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Abba ya tabbatar da korar Aminu Ado Bayero, ya sanya hannu a dokar da ta rusa su

Hakan ya biyo bayan rusa masarautun da majalisar jihar ta yi tare da wargaza dukkan dokokin da ke cikinta.

Gwamnati ta rusa masarautun Kano 5

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Kano ta rusa masarautun jihar guda biyar da aka kirkira a 2019.

Majalisar ta dauki matakin ne domin dawo da tsarin da ake a da kafin gwamnatin Abdullahi Ganduje ta sauya dokar.

Daukar wannan mataki yasa aka fara jita-jitar dawo da Muhammadu Sanusi II kan kujerarsa bayan tsige shi a 2020.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.