Sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya shiga gidan sarauta

Sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya shiga gidan sarauta

- Sabon Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya koma gidan sarauta a daren ranar Laraba, 11 ga watan Maris

- Bayero ya shiga Soron Shekara sannan daga nan ya shiga Soron Ingila, wanda nan ne gidansa a cikin masarautar inda ya ke karban gaisuwa daga ahlin gidan sarauta da sauran sarakunan gargajiya

- Za kuma a gudanar da hawan daba na musamman domin karrama sarkin, tare da addu’o’i na musamman don zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano

Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya koma gidan sarauta a daren ranar Laraba, 11 ga watan Maris, yan sa’o’i kadan bayan ya karbi takardar kama aiki daga wajen gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Daruruwan al’umman Kano sun isa gidan sarautar domin shaida al’ada na shigar sarki gidan sarautar ta wata kofar tarihi, wacce ta ke al’ada da ke tabbatar da daura Bayero a matsayin sarki.

An gano fadawa da masu rawar gargajiya yayinda sarkin ke shiga Soron Shekara sannan daga nan ya shiga Soron Ingila, wanda nan ne gidan sarki a cikin masarautar inda ya ke karban gaisuwa daga ahlin gidan sarauta da sauran sarakunan gargajiya.

Sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya shiga gidan sarauta

Sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya shiga gidan sarauta
Source: Facebook

Sabon sarkin wanda ya kasance mai digiri a fannin sadarwa daga jami’ar Bayero, kuma kwararren matukin jirgi, Aminu Ado Bayero ya shafe mafi akasarin rayuwarsa yana yiwa masarautar Kano hidima.

Ya riki mukamai daban-daban da suka hada da Turaki, Sarkin Dawakin Tsakar Gida, da kuma Wambai na Kano.

Ya kuma kasance sarkin Bichi kafin a nada sa a matsayin sarkin Kano a yanzu.

A kwanaki masu zuwa, Bayero zai ci gaba da aiwatar da wasu al’adu da suka hada da jagorantar zaman majalisar sarakunan gargajiya na Kano.

KU KARANTA KUMA: Tuna baya: Hotunan korarren sarkin Kano Sanusi Lamido da matarsa ta farko Sadiya Ado Bayero

Za kuma a gudanar da hawan daba na musamman domin karrama sarkin, tare da addu’o’i na musamman don zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel