Jarirai 21,000 Na Mutuwa a Kowane Wata a Najeriya, Gwamnan Kaduna Ya Fadi Dalili
- Gwamnatin Kaduna ta gina cibiyar PSA ta sarrafa iskar Oxygen a asibitin tunawa Yusuf Dantsoho domin amfanin jarirai
- Wannan kuwa na zuwa ne yayin da Gwamna Uba Sani ya ce kimanin jarirai 700 ne ke mutuwa kowace rana a Najeriya
- A cewar gwamnan jihar na Kaduna, wannan cibiyar ta PSA za ta taimaka wajen rage yawan mace-macen jarirai a Kaduna
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Mai girma Uba Sani, ya ce kimanin jarirai 700 ne ke mutuwa kowace rana a Najeriya.
Kaduna ta ginawa jarirai cibiyar Oxygen
Gwamnan Kaduna ya nuna damuwa kan kalubalen da kasar ke fuskanta na yawaitar mace-macen mata da kananan yara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da wani sabon ginin cibiyar PSA ta sarrafa iskar oxygen da aka gina a asibitin Yusuf Dantsoho.
Gwamna Uba Sani, wanda ya samu wakilcin mataimakiyarsa, Dakta Hadiza Balarabe, ya ce wadannan ayyukan za su taimakawa kokarin jihar na magance matsalar mace-macen jarirai.
Hanyar rage mace-macen jarirai a Kaduna
Gwamna Sani ya bayyana cewa jihar Kaduna ce ta fi kowacce jiha yawan mace-macen jarirai a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Ya ce sabuwar cibiyar da aka kaddamar za ta rika ba jariran da ke tsakanin kwanaki 0 zuwa 28 kulawa, da samar da muhimman abubuwan taimakawa rayuwar yara da uwayensu.
Gwamnan ya kara da cewa gina cibiyar iskar iskar din za ta tabbatar da isar da iskar oxygen ga sashen jarirai da sauran wurare a fadin jihar.
Mutuwar jarirai: Gwamnati ta magantu
Wata jami’ar ma’aikatar lafiya ta tarayya, Misis Evelyn Agbanyim ta taba cewa sama da jarirai 700 ne ke mutuwa a kullum a Najeriya saboda rashin tsaftar da kuma kamuwa da cututtuka a lokacin haihuwa.
Ta bayyana manyan abubuwan da ke haifar da mutuwar jarirai a Najeriya da suka hada da karancin nauyin haihuwa, ciwon nakuda da kamuwa da cututtuka, in ji rahoton Vanguard.
A cewar ta, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar yin wani gangami na wayar da kan masu ruwa da tsaki a kasar sakamakon halin da ake ciki.
Kotu ta tube rawanin babban sarki
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotu a jihar Ondo, ta tsige Oba Michael Adetunji Oluwole daga sarautar 'Sarkin Ute'.
Wannan na zuwa ne bayan da aka shafe shekaru 29 ana takaddamar shari'a kan cancantar zaman Oba Michael a matsayin Sarkin na Ondo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng