Nigerian news All categories All tags
Najeriya ce kasa ta 11 cikin jerin kasashen da rayuwa keda tsananin wahala

Najeriya ce kasa ta 11 cikin jerin kasashen da rayuwa keda tsananin wahala

- Asusun Tallafawa Karatun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF a wani sabon rahoto mai taken “Kowane Yaro a Raye” ta bayyana cewa: Adadin yawan jariran da je mutuwa a kowace rana na ci gaba da hauhawa a fadin duniya

- Rahoton ya nuna Nigeria a matsayin kasa ta Goma sha daya (11) dake fuskantar yawaitar mace macen jarirai, da kiyascin mutuwar jarirai Ashirin da Tara (29) a kowace haihuwa 1,000

- A kowace shekara, akalla jarirai Miliyan Biyu da Dubu Dari Shida ne ke kasa wuce watan farko na haihuwarsu. Miliyan daya daga cikinsu na mutuwa ne a ranar farko da aka haifesu

Asusun Tallafawa Karatun Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF a wani sabon rahoto mai taken “Kowane Yaro a Raye” ta bayyana cewa: Adadin yawan jariran da je mutuwa a kowace rana na ci gaba da hauhawa a fadin duniya—hakan yafi faruwa a kasashen da ke kan ganiyar ci gaba.

Rahoton ya nuna Nigeria a matsayin kasa ta 11 dake fuskantar yawaitar mace macen jarirai, da kiyasin mutuwar jarirai 29 a kowace haihuwa Dubu Daya 1,000.

Najeriya ce kasa ta 11 cikin jerin kasashen da rayuwa keda tsananin wahala

Najeriya ce kasa ta 11 cikin jerin kasashen da rayuwa keda tsananin wahala

Samun kyakkyawar rayuwa na farawa ne da samun ingantaccn farko mai cike da koshin lafiya. Sai dai abin takaicin shine, da yawan kananan yara a Nigeria basa samun wannan kyakkyawan mafari a rayuwarsu” cewar Mohammed Fall, wakilin Asusun UNICEF a Nigeria.

KARANTA WANNAN: Majasilar dattijai ta bayyana wadanda ke jawo cikas a zartar da kasafin kudin shekarar nan

Mohammed Fall yaci gaba da cewa: “Rahotannin da tsarin bincike na MICS suka tattara, ya nuna mana cewa matsalar na ci gaba da hauhawa, amma akwai bukatar daukar matakan gaggawa don baiwa yan Nigeria damar cimma Muradun Karni (SDGs). Bai kyautu a ce kasar ta kasa ceto rayukan jariran da ake haihuwa a kowace ran aba.”

A kowace shekara, akalla jarirai Miliyan Biyu da Dubu Dari Shida ne ke kasa wuce watan farko na haihuwarsu. Miliyan daya daga cikinsu na mutuwa ne a ranar farko da aka haifesu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel