An Ƙara Samun Matsala Yayin da Gwamnatin Tinubu Ta Faɗi Sabon Tayin Mafi Ƙarancin Albashi
- Gwamnatin tarayya ta sake gamuwa da cikas daga ƴan kwadago bayan ta gabatar da tayin N57,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi
- Rahotanni sun nuna ƴan kwadago a Najeriya sun yi fatali da tayin a karo na uku amma sun rage bukatarsu daga N615, 000 zuwa N497, 000
- NLC da TUC sun jaddada cewa bai kamata watan Mayu ya ƙare ba tare da ma'aikata sun san sabon mafi ƙarancin albashi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarshin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta gabatar da sabon tayin mafi ƙarancin albashin ma'aikata ga ƴan kwadago.
Gwamnatin Najeriya ta ƙara N3,000 daga N54,000 da ta gabatar a baya, inda ta miƙa sabon tayi na N57,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.
The Nation ta ce an samu tabbacin miƙa sabon tayin daga bakin wata majiya da ta halarci taron kwamitin mafi ƙarancin albashi a birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan kwadago sun yi watsi da tayin albashi
Rahoton Channels tv ya tattaro cewa manyan ƙungiyoyin kwadago sun sake yin fatali da sabon tayin gwamnatin tarayya na N57,000.
Amma mutumin ya ce yan kwadagon sun sassauta buƙatarsu daga N615, 000 zuwa N497, 000 a matsayin mafi ƙarancin albashin da suke fatan gwamnati ta biya.
"Gwamnati ta sake gabatar da tayin N57,000 amma ƴan kwadago suka nuna ba su amince ba nan take, sun rage bukatarsu zuwa N497,000,"
- Majiyar.
A ranar Talata ne aka ci gaba da tattaunawa kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa domin baiwa gwamnoni damar halartar taron.
Kungiyoyin kwadago sun fusata da gwamnati
Ranar Larabar da ta gabata gwamnati ta gabatar da N48,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi wanda ƴan kwadago suka yi fatali da shi a karon farko, suka fice daga taron.
Bayan haka gwamnati ta ƙara adadin zuwa N54,000 wanda shi ma ƴan kwadagon ba su yi jinkiri ba, suka yi watsi da shi.
A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a ranar Litinin, NLC da TUC sun jaddada cewa ya kamata a kammala tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi a karshen watan Mayu.
Bola Tinubu ya yi sababbin naɗe-naɗe
A wani rahoto kuma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauya shugabancin wasu hukumomin gwamnatin tarayya guda biyu ranar Laraba
Tinubu ya amince da naɗin Injiniya Chukwuemeka Woke, da Dokta Adedeji Ashiru a matsayin waɗanda za su jagoranci hukumomin tarayyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng