Bidiyo da hotunan yara masu kada kuri’a: Aikin yaran Kwankwaso ne - Ganduje
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da hotuna da bidiyon da ya watsu a kafafen sada ra’ayi da zumunta da ke nuna kananan yara yan kasa da shekaru 18 suna kada kuri’a.
Ya bayyana cewa wannan aikin yan adawa ne kawai domin bata sunan gwamnatinsa.
Yayinda yake tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa Aso Villa, gwamna Ganduje wannan kaidin magoya bayan tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso ne kawai.
A jawabinsa yace: “Ku tambayi yan kasashen wajen da suka zo sa ido a zaben, ai sun yi hira da manema labarai bayan zagayawarsu. Ku tambaye su, sun shiga layi sun kada kuri’a? Ba zai yiwu ba. Saboda haka, ba mu da lokacin kace-nace dasu”.
Kuma game da rikicinsa da Kwankwaso, Ganduje ya nuna cewa ana son a dinga masa juyin waina ne kuma ba zai yarda ba.
KU KARANTA: Gwamann jihar Bauchi ya kaiwa Maikanti Baru ziyara Abuja
Yace: “Kun san yadda yanayin mulki yake. Bai yiwuwa a ce ka na mulki amma ba kai ke mulkin ba, wani can ne zai rika jujjuya ka daga waje.”
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng