Rikici Ya Kaure da Aka Bindige Ɗan Sanda a Tsakiyar Kasuwar Jos

Rikici Ya Kaure da Aka Bindige Ɗan Sanda a Tsakiyar Kasuwar Jos

  • An shiga fargaba bayan bindige wani jami'in ɗan sanda a cikin kasuwa a karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Plateau
  • Lamarin ya faru ne a yau Laraba 22 ga watan Mayu yayin da jami'an tsaro suka shiga kasuwar domin tabbatar da doka
  • Hukumar kula da ci gaban birane da hadin guiwar jami'an tsaro sun shiga kasuwar domin hana cinikayya a bakin titi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Wani jami'in dan sanda ya gamu da ajalinsa bayan an bindige shi a cikin kasuwa.

Ɗan sandan ya rasa ransa ne a tsakiyar kasuwar 'Terminus' da ke Jos ta Arewa a jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Yayin da ya ke jimamin mutuwar mahaifiyarsa, Kotu ta tausayawa Abba Kyari

An bindige wani ɗan sanda har lahira a kasuwa a cikin Jos
Wani ɗan sanda ya rasa ransa yayin da aka bindige shi a kasuwar Jos. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Yaushe aka bindige ɗan sanda a Jos?

Lamarin ya faru ne da safiyar yau Laraba 22 ga watan Mayu yayin da jami'an tsaro ke kokarin hana mutane cinikayya a bakin titi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu masu siyar da kaya a kasuwar sun tabbatarwa jaridar Punch yadda lamarin ya faru na kisan ɗan sandan.

Sai dai sun ba da mabambantan bayanai kan ainihin wadanda suka yi kisan da ya jefa mutane cikin fargaba.

An bayyana yadda ɗan sandan ya mutu

Wata mai suna Amina Mohammed ta ce wani jami'in dan sanda ne ya yi harbin yayin kwantar da tarzoma inda aka samu akasi ya bindige dan uwansa.

"Jami'an tsaro da hukumar Metropolitan Development Board sun shigo kasuwar domin hana cinikayya da ake yi kan hanya."
"Ka san suna fuskantar kalubale daga ƴan kasuwar kan matakin, wani ɗan sanda ya yi harbin inda aka yi rashin sa'a ya bindige dan uwansa."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da jami'in kwastam a Abuja

- Amina Mohammed

Bindigar 'dan sanda ko miyagu?

Sai dai wani mai suna Haruna ya ce ana zargin wasu miyagu ne da suka ce ba za su bar kasuwanci a wurin ba da kisan ɗan sandan.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Alfred Alabo ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun kaddamar da bincike domin gano gaskiya.

Yan bindiga sun hallaka mutane a Plateau

Kun ji cewa ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Zurak da ke gundumar Bashar a karamar hukumar Wase a jihar Plateau.

Rahotanni sun tabbatar cewa an kashe mutane sama da 40 yayin harin ciki har da jami'an tsaron sa-kai na ‘yan banga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel