Shugaba Tinubu Ya Nada 'Dan Arewa a Matsayin Sabon Shugaban Hukumar FRSC

Shugaba Tinubu Ya Nada 'Dan Arewa a Matsayin Sabon Shugaban Hukumar FRSC

  • Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) ta samu sabon shugaba bayan kammala wa'adin tsohon shugabanta Dauda Ali Biu
  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin ACM Shehu Mohammed a matsayin sabon wanda zai jagoranci hukumar har na tsawon shekara huɗu
  • Naɗin na sabon shugaban hukumar ta FRSC wanda ya yi daidai da tanadin dokar da ta kafa hukumar zai fara aiki ne daga ranar, 20 ga watan Mayun 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin ACM Shehu Mohammed a matsayin shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC).

Hakan na ƙunshe ne a cikin takardar naɗin mai ɗauke da kwanan watan 20 ga watan Mayu wacce sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya rattaɓawa hannu.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya tsige shugaban OORBDA, ya naɗa mutum 2 a manyan muƙamai

Shugaba Tinubu ya nada sabon shugaban FRSC
Shugaba Tinubu ya nada Shehu Mohammed matsayin sabon shugaban hukumar FRSC Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Takardar ta bayyana cewa naɗin ya yi daidai da tanadin sashe na 7 (1) na kuɗirin dokar kafa hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa na shekarar 2007, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe shugaban FRSC zai fara aiki?

Naɗin na Shehu Mohammed a matsayin sabon shugaban hukumar ta FRSC zai fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Mayun 2024.

Shehu Mohammed ya karɓi ragamar shugabancin hukumar FRSC daga hannun Dauda Ali Biu, wanda ya kammala wa'adinsa.

Naɗin Shehu Mohammed zai kwashe shekara huɗu ne wanda za a iya sabuntawa a ƙarshen wa'adinsa kamar yadda dokokin hukumar suka tanada, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da wannan.

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen, ya tabbatar da naɗin cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 22 ga watan Mayun 2024.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa Kwankwaso, Atiku da Peter Obi ba za su kai labari ba a zaɓen 2027"

Tinubu ya ba surukinsa muƙami

A baya rahoto ya zo cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin surukinsa, Oyetunji Oladimeji Ojo, a matsayin sabon shugaba kuma direkta na Hukumar Gidaje na Tarayya (FHA).

Oyetunji Oladimeji Ojo wanda tsohon dan majalisar wakilai na tarayya ne, yana auren babban ƴar Shugaba Tinubu, Misis Folashade Tinubu-Ojo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel