NAHCON Ta Faɗi Dalilin Rashin Fara Jigilar Alhazan Kano da Wasu Jihohi 6, Ta Gama da Nasarawa
- Yau Laraba za a fara jigilar alhazan jihohin Kano, Kaduna da wasu jihohin Arewa zuwa ƙasa mai tsarki bayan kammala kwashe na Nasarawa
- Hukumar NAHCON ce ta bayyana haka a wata sanarwa da Fatima Sanda Usara, mai magana da yawun hukumar ta rattaɓawa hannu
- Ta shawarci maniyyata su kwantar da hankalinsu domin duk wanda ya fara tafiya shi zai fara dawowa gida bayan kammala aikin hajji
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta sanar da cewa ta kammala jigilar maniyyatan jihar Nasarawa zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar fitar ranar Laraba, 22 ga watan Mayu, 2024.
Ta ce maniyyatan jihohin Kaduna, Kano, Borno, Yobe da Adamawa za su fara tashi zuwa ƙasa mai tsarki yau Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Abin farin ciki, jihar Nasarawa ce ta farko da ta kammala jigilar maniyyatan ta 1,794 zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajjin bana 2024.
"Jiya Talata da daddare ake tsamnanin jihar Oyo da hukumomin tsaro za su kammala kwashe maniyyatan su, sawu ɗaya ya rage ma kowanen su."
- Fatima Usara.
Za a fara kwashe alhazan Kano da Kaduna
Mai magana da yawun NAHCON ta ƙara da cewa a halin yanzun za a shiga mako na biyu bayan fara jigilar alhazan Najeriya zuwa Saudi Arabia.
Ta ce jihohin da za su fara jigilar alhazan su yau Laraba sun hada da jihohin Kaduna, Yobe, Kano, Adamawa, Borno, da Sokoto da kuma Filato.
Hukumar ta kuma buƙaci maniyyatan da su kwantar da hankalinsu kan rashin kwashe su da wuri domin NAHCON tana da tsarin na farkon tafiya shi ne na farko a dawowa.
Fatima ta ce kowane maniyyaci zai kwashe kwanaki daidai da kowa a ƙasa mai tsarki, babu wanda zai fi wani.
Ta kuma ƙara da cewa NAHCON ta samu nasarar jigilar alhazai sama da 10,000 kawo yanzu kuma babu jirgin da aka soke bayan kammala shirin tashinsa.
Naira ta kara farfaɗowa
A wani rahoton kuma, an ji kimar Naira ta ƙara sama a kasuwar hada-hadar gwamnati ranar Talata sa'o'i 24 bayan kuɗin Najeriya sun rikita Dalar Amurka.
Rahoton FMDQ na ranar Talata ya nuna cewa Naira ta tashi da N3.31 inda aka yi musayar kowace Dalar Amurka kan N1,465.68.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng