Gombe: Gwamna Dankwambo ya nada sabon Amirul Hajj na jihar Gombe

Gombe: Gwamna Dankwambo ya nada sabon Amirul Hajj na jihar Gombe

- Gwamnatin jihar Gombe ta nada tawagar Amirul Hajj na 2017

- Tsohon Jakadan Najeriya a kasar Kuwait, Haruna Garba zai shugabanci tawagar

- Tawagar Amirul Hajj ta kunshi mutane 16

Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ya nada mutane 16 a matsayin tawagar Amirul Hajj na shekara ta 2017 a jihar.

Tawagar za ta kasance a karkashin shugabancin Haruna Garba, wani tsohon Jakadan Najeriya a kasar Kuwait.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, tawagar Amirul Hajj sun hada da; Hon. Aishatu MB Ahmed, Hon. Usman Muhammad Ribadu, Hon. Abdullahi Pindiga, Hon. Miji Tilde, Hon. Justice Abubakar Jauro, Hon. Justice Adamu Usman, Sheik Adamu Dokoro, Sheikh Hamza Adamu Abdulhamid.

Gombe: Gwamna Dankwambo ya nada sabon Amirul Hajj na jihar Gombe
Masallacin Ka'aba

Sauran su ne; Malam Salisu Muhammad Gombe, Malam Bashir Ladan, Dr. Muhammad Lawan, Alh. Gambo Isari, Alh. Idi Maipachi, Abdullahi DanGombe Filiya da Sheik Zakariyya Ajiya wanda shine aka nada a matsayin sakataren tawagar.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya tayi ma jihohin Najeriya ruwa biliyoyin nairori (KARANTA)

A cikin wata sanarwa dauke da sanya hannun mukaddashin sakataren gwamnatin jihar, James Pisaghi JP, gwamna Dankwambo ya bukaci tawagar da nauyin da suka hada da; sa ido ga ayyukanin hajjin bana na 2017 da kuma warware duk wani matsala da zai iya kunno kai a lokacin aikin hajji da kuma taimakawa kokarin hukumar kula da Alhazai na kasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel