Gwamnatin Kano ta Sayawa 'Yan Majalisa Motocin Alfarma kan N2.6bn

Gwamnatin Kano ta Sayawa 'Yan Majalisa Motocin Alfarma kan N2.6bn

  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta gwangwaje 'yan majalisar jihar da dalla-dallan motoci da kudinsu ya kai N2.6bn domin su ji dadin gudanar da aikinsu ga wadanda su ka zabe su
  • Gwamnatin ta sayi motocin kirar Toyota Fortuner guda 41 inda kowane dan majalisa zai samu mota guda wacce kudinta ya kai N68m, tuni wasu daga wakilan su ka adana motarsu a gidajensu
  • Shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagagi ya tabbatar da sayen motocin inda ya ce 'yan majalisar sun cancanci hakan, yayin da wadanda ba su karba ba su ke jiran ta su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa

Jihar Kano- Gwamnatin Kano ta sayawa ‘yan majalisar jihar motocin alfarma kirar Toyota Fortuner guda 41.

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Bola Tinubu ta jefa Najeriya cikin tsaka mai wuya," Dattijon Arewa

Rahotanni sun bayyana cewa an sayi kowacce mota a kan ₦68m, wanda kudin baki daya ya tashi a kan ₦2.6bn.

Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Kano ta rabawa 'yan majalisar jiha tsala-tsalan motocin ₦2.6bn Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Punch News ta wallafa cewa shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagagi ne ya tabbatar da sayen tsala-tsalan motocin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin gwamnatin Kano na sayen motocin

Shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagagi ya ce an sayi motocin ne domin 'yan majalisa su ji dadin aiki.

A cewarsa, wakilan al'ummar sun cancanci yin aikin hidimtawa jiha cikin nutsuwa.

Solacebase ta ruwaito cewa tuni wasu 'yan majalisar su ka karbi motocinsu, yayin da wasu ke dakon karasowar ta su.

An fara raddi kan sayen motocin

Mashawarcin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmed ya bayyana mamaki kan sayen motocin da gwamnatin Kano ta yi.

A sakon da ya wallafa ta shafinsa na X, tsohon mashawarcin ya ce bai san me zai yi ba, murna ko taya talakawa sama da miliyan 20 bakin ciki.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Babbar mota ta murkushe motoci 4, mutane da yawa sun mutu a jihar Imo

Kungiya ta wanke tsohon gwamnan Kano

A baya mun ruwaito mu ku cewa wata kungiya mai zaman kanta ta wanke tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje daga zargin rashawa.

Gwamnatin Kano mai ci karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ce ta fara binciken gwamnan bisa zargin almundahana da badakalar kudin talakawan jihar a gaban kotu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.