Afonja: Tsohon Minista a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Bayan Ya Yi Haɗari

Afonja: Tsohon Minista a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Bayan Ya Yi Haɗari

  • Tsohon ministan kwadago kuma tsohon shugaban First Bank, Prince Ajibola Afonja ya riga mu gidan gaskiya a asibitin UCH
  • Rahotannin da suka fito ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, sun nuna cewa Afonja, wanda ake kira IDS ya mutu ne ranar Lahadi
  • Tuni dai aka fara ta'aziyyar rasuwar tsohon ministan, wanda ya rasu bayan samun raunuka a wani hatsari da ya rutsa da shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Tsohon ministan kwadago a gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙasa, Prince Ajibola Afonja, ya riga mu gidan gaskiya.

Afonja, wanda ya riƙe kujerar minista a mulkin rikon ƙwarya karkashin Chief Ernerst Sonekan, ya mutu ne a daren ranar Lahadi, 19 ga watan Mayu, 2024.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya tsoma baki kan rigimar Ministan Tinubu da gwamnan PDP

Tsohon minista, Prince Ajibola Afonja.
Allah ya yi wa. tsohon minista, Prince Ajibola Afonja rasuwa Hoto: Adeleke Wasiu Adewale
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro, tsohon ministan ya cika ne a asibitin jami'ar jihar (UCH) da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A 'yan kwanakin nan ana ta samun labarin mace-mace a jihohin Najeriya.

Prince Afonja, tsohon shugaban First Bank, ya rasu yana da shekaru 82 a duniya kamar yadda jaridar Punch ta kawo a rahotonta ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, 2024.

Yadda Ajibola Afonja ya rasu daga hadari

Tsohon ɗan kwadagon, wanda ya fi shahara da sunansa na kamfani watau IDS a mahaifarsa da ke jihar Oyo, ya gamu da hatsarin mota kuma ya ji raunuka da dama.

Daga nan aka garzaya da shi asibitin UCH da ke Ibadan, wanda a ƙarshe rai ya yi halinsa.

Shugaban ƙungiyar masu kishin Oyo Taiwo Adebayo, ya tabbatar da mutuwar tsohon ministan a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a daren ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Ebrahim Raisi: Muhimman abubuwa 5 da baku sani ba kan shugaban ƙasar Iran da ya rasu

Sanarwar mutuwar tsohon minista

Ya bayyana marigayi Afonja a matsayin mai ƙoƙarin haɗa kan kasa, inda ya ce:

"A wannan rana mai cike da alhini, muna miƙa sakon ta'aziyya bisa rasuwar Prince Ajibola Afonja."
"Ayyukansa na alheri da karamci sun tallafi rayuwar mutane da dama kuma za a yi kewar rashinsa sosai."

Babbar mota ta halaka mutane a Imo

A wani rahoton kuma wata babbar mota ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a jihar Imo biyo bayan yadda ta murkushe wasu motocin bas guda hudu.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da yadda lamarin ya faru da kuma irin tashin hankalin da dangi suka shiga bayan hadarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262