Harin Masallacin Kano Ya Haifar da Marayu da Zawarawa da Dama

Harin Masallacin Kano Ya Haifar da Marayu da Zawarawa da Dama

  • A yayin da ake cigaba da zaman makoki bayan harin da aka kai Kano an bayyana adadin marayu da zawarawa da lamarin ya haifar
  • Wani shugaba a yankin Abasawa ne ya bayyana adadin tare da cewa adadin waɗanda suka mutu sanadiyyar harin na cigaba da karuwa
  • Rahotanni sun kara tabbatar da cewa dukkan waɗanda harin ya ritsa da su yan uwa ne na jini kuma suna zaune a wuri guda tsawon shekaru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

jihar Kano - A yayin da ake cigaba da samun karuwar mutuwar mutane a harin da aka kai masallaci a jihar Kano, an lissafa adadin marayu da lamarin ya haifar.

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

Kano attack
An samu marayu kimanin 100 bayan harin masallaci a Kano. Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Wadanda harin ya ritsa da ilalansu suna zaman makoki a yankin Gidan Goro da ke Larabar Abasawa a karamar hukumar Gazawa.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa a halin yanzu adadin waɗanda suka mutu sanadiyyar harin sun kai kimanin mutum 17.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kai hari a masallacin Kano

Legit ta ruwaito cewa a ranar Laraba da ta wuce ne wani mutum mai suna Shafi'u ya kunna wuta kan masallata da asuba.

Lokacin da rundunar yan sandan jihar Kano ta kama matashin ya bayyana cewa saboda rikicin kudin gado da suke ne ya kunna wuta a masallacin.

Halin da ake ciki a Abasawa

A halin yanzu dai garin Abasawa na rikice da jimami kasancewar ana cigaba da samun karin wadanda suka mutu cikin wanda harin ya ritsa da su.

Bincike ya nuna cewa a halin yanzu harin ya haifar da sama da marayu akalla 100 da zawarawa 13 a garin a cewar rahoton Aminiya.

Kara karanta wannan

Kwara: Sun fadi gaskiya bayan cafke likita da wasu da zargin satar mahaifa da cibiyar jariri

Kano: Jawabin wani shugaba a Abasawa

Wani shugaba a yankin Abasawa, Musa Muhammad ya tabbatar wa manema labarai cewa dukkan waɗanda harin ya ritsa da su yan uwa ne na jini kuma suna zaune a wuri ɗaya.

Musa Muhammad ya kuma kara da cewa a cikin mutanen da harin ya afkawa guda hudu ne kawai ba su da aure, kuma cikin mutanen akwai mutum daya da ke da 'ya'ya sama da 19.

Ganduje ya magantu kan harin Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jajantawa waɗanda harin da aka kai masallaci ya shafa a jihar Kano ranar Laraba da ta gabata.

Shugaban APC na ƙasa ya buƙaci masu hannu da shuni su taimakawa iyalan waɗanda suka rasu da waɗanda ke kwance suna jinya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng