Tinubu Ya Sake Ba Babban Mai Magana da Yawunsa, Ajuri Ngelale Sabon Mukami
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Ajuri Ngelale matsayin wakilin shugaban kasa na musamman kan ayyukan sauyin yanayi
- Haka zalika, Ngelale ne sakataren sabon kwamitin mutane 25 da aka kafa kan shirin tattalin arziki na Green Economic Initiatives (GEI)
- Kafin wannan nadin, Ajuri Ngelale shi ne mai ba Tinubu shawara na musamman kan harkokin yada labarai
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi sabon nadi ga Ajuri Ngelale, mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai.
Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
An nada Ngelale a matsayin wakilin shugaban kasa na musamman kan ayyukan sauyin yanayi da kuma sakataren sabon kwamitin mutane 25 da aka kafa domin sa ido kan shirin tattalin arziki na Green Economic Initiatives (GEI).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aikin da kwamitin zai rika yi
A cewar sanarwar, Tinubu ya kafa kwamitin ne a wani muhimmin mataki na tabbatar da kudurin gwamnatin sa kan sauyin yanayi da kuma shirin GEI, rahoton jaridar Daily Trust.
Shugaban kasa Bola Tinubu shine shugaban kwamitin.
Sanarwar da Segun Imohiosen, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ofishin SGFs ya sanya wa hannu a madadin Akume ta ce:
"Kwamitin shugaban kasa kan ayyukan yanayi da Green Economic, zai kula ne da duk manufofi da shirye-shiryen gwamnati kan ayyukan sauyin yanayi da shirin GEI."
Mambobin kwamitin shirin shugaban kasa
Baya ga shugaba Tinubu da Ngelale, PM News ta ruwaito sauran mambobin kwamitin sun hada da ministan muhalli, Balarabe Abbas Lawal a matsayin mataimakin shugaba.
Sauran sun hada da: Shugaba, InfraCorp, Lazarus Angbazo; Shugaban NCCC, Salisu Dahiru; Shugaban ICRC, Michael Ohiani; Shugabar NIPC, Aisha Rim; da shugaban NSIA, Aminu Umar-Sadiq.
Sauran su ne: Shugaban NAGGW, Yusuf Maina-Bukar; Shugaban ECN, Abdullahi Mustapha; Shugaban REA, Abba Abubakar Aliyu; da shugaban CrediCorp, Abba Uzoma Nwagba.
Shirin Tinubu kan maye fetur da CNG
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki wasu matakai a makon da ya gabata, da suka fito da aniyarsa ta janye Najeriya daga dogara da fetur zuwa makamashi.
A yayin da Tinubu ya umarci hukumomi, ma'aikatu da mukarraban gwamnati da su daina sayo motoci masu amfani da fetur, Tinubu ya kuma aiwatar da abubuwan da za su samar da gas.
Asali: Legit.ng