Ta'addanci, sauyin yanayi, rashin tsaro, manyan kalubale ne garemu, Buhari
- Muhammadu Buhari, shugaban kasar Najeriya, yace ta'addanci, rashin taro da sauyin yanayi manyan kalubale ne a duniya
- Shugaban ya sanar da hakan ne yayin da ya karba jakadun kasashe daban-daban na duniya a fadarsa dake Abuja
- Yayi kira garesu da a hada karfi da karfe wurin fattattakar dukkan matsalolin da suka addabi duniya a tare
Shugaban kasa M,uhammadu Buhari yace ta'addanci, mayar da jama'a 'yan gudun hijira da sauyin yanayi manyan kalubale ne ga jama'a da alakar dake tsakaninsu.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ya ce akwai matukar amfani kasashen duniya su yi aiki tare domin samo hanyoyin da ya dace wurin shawo kan wadannan kalubalen.
Ya sanar da hakan ne yayin jawabi a wani shagalin karbar wasikar jinjina a gidan gwamnati dake Abuja, inda yace wannan kalubalen manyan matsaloli ne ga al'umma.
KU KARANTA: Tsarikan makiyaya da kake fadi ba kamar kalmashe daloli bane, Miyetti Allah ga Ganduje
KU KARANTA: Sojoji sun sheke 'yan bindiga 2 yayin da suka kai samame maboyarsu a Kaduna
Buhari ya karba wasikar ne daga babban kwamishinan The Gambia, Mohamadou Musa Njie; jakadan kasar Korea ta kudu, Kim Young-Chae; jakadan Slovak, Tomas Felix; Babban kwamishinan Australia, John Gerard Donnelly; babban kwamishinan Bangladesh, Masudur Rahman da jakadan Guinea Bissau, Jaao Ribeiro Butiam Co.
Buhari yayi kira ga jakadun da su dage wurin aiki tukuru da zai tabbatar da ingantacciyar alaka tare da mayar da hankali wurin shawo kan kalubelen da ake fuskanta.
Yace annobar korona da ta addabi duniya har yanzu ita ce babban kalubale ga lafiya amma illar da tayi ga tattalin arziki ba kadan bane.
A wani labari na daban, kungiyar gamayyar masana tsaro ta Najeriya (CCNSE) a ranar Laraba ta caccaki hafsoshin tsaron kasar nan da suka zabi su dinga aiki daga Abuja. Sun bukacesu da su koma yankin arewa maso gaba, tsakiyar inda rashin tsaro yafi kamari a kasar nan.
Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar ta nuna damuwarta ta yadda watanni biyu da hawan sabbin hafsoshin tsaron amma koyaushe rashin tsaro kara kamari yake yi.
Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Otedola Adekunle da sakataren kungiyar na kasa, Dr Chris Aklo, sun kalubalanci shugabannin tsaron da su tashi su tsaya kan nauyin da aka dora musu, ganin cewa watanni biyu sun isa a fara ganin alamun shawo kan matsalar tsaro.
Asali: Legit.ng