An Shiga Jimami Yayin da Dattijo Mai Shekaru 50 Ya Mutu Yana Tsaka da Kallon Ƙwallo
- Abin tausayi ya faru a jihar Lagos yayin da wani dattijo mai shekaru 50 ya rasu yayin da yake kallon kwallo a gidan shan barasa
- Dattijon wanda ba a bayyana sunansa ba ance yana yawan zuwa gidan kallon kwallon da sauran lamura kafin afkuwar lamarin
- Kakakin rundunar yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbayar da faruwar lamarin inda ya ce an kwashi gawarsa zuwa asibiti
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - An shiga jimami bayan rasuwar wani dattijo mai shekaru 50 a duniya a jihar Lagos.
Ana zargin dattijon ya rasu yayin da yake kallon kwallo a wani gidan shan barasa da ke kan hanyar Lagos zuwa Abeokuta.
Yaushe dattijon ya mutu a Lagos?
Marigayin wanda ba a bayyana sunansa ba an tabbatar cewa yana zuwan gidan shan barasan a lokuta dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Vanguard ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar 15 ga watan Mayu bayan marigayin ya je wurin domin kallon kwallo.
Wata majiya ta ce dattijon na zaune ne a kan kujera kamar yana bacci amma da aka zo tashinsa aka samu rai ya yi halinsa, Punch ta tattaro.
Ƴan sanda sun yi martani a Lagos
Kakakin rundunar ƴan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Asabar 18 ga watan Mayu.
Hundeyin ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 a ranar 15 ga watan Mayu bayan mai gidan shan barasan ya kawo korafi a ofishin ƴan sanda da ke Elere.
Ya ce rundunar ta samu zuwa wurin da lamarin ya faru inda aka tabbatar ya mutu a kan kujerar ba tare da wani alamar hayaniya da aka yi da shi ba.
"An dauki gawarsa zuwa babban asibitin Mainland da ke Rusty Yaa domin gudanar da bincike mai zurfi."
"Muna ci gaba da neman iyalansa domin tabbatar da mika shi gare su."
- Benjamin Hundeyin
Sanwo-Olu ya tafka babban rashi
A wani labarin, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanar da mutuwar mataimakin shugaban ma'aikatansa, Gboyega Soyannwo.
Sanwo-Olu ya ce tabbas marigayin mutumin kirki ne kuma ya wuce ma'aikacinsa sai dai ɗan uwa saboda irin yadda suka zauna lafiya da juna.
Asali: Legit.ng