'Yan Bindiga: Gwamnonin Arewa Sun Nemi Taimakon Majalisar Dinkin Duniya

'Yan Bindiga: Gwamnonin Arewa Sun Nemi Taimakon Majalisar Dinkin Duniya

  • Gwamnonin Arewa maso yamma sun mika kokon bara ga majalisar dinkin duniya (UN) domin magance matsalolin yankinsu
  • Shugaban gwamnonin yankin, Dikko Umaru Radda ya lissafa matsalolin da yankin ya fi fama da su domin ba su kulawa ta musamman
  • Majalisar ɗinkin duniya ta nuna jin dadin yadda gwamnonin suka kai mata ziyara tare da bayyana matakin da za ta dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Biyo bayan matsalar yan bindiga da ta addabi yankin Arewa maso yammacin Najeriya, gwamnonin yankin sun nemi agaji daga majalisar dinkin duniya.

Gwamnonin arewa maso yamma
Gwamnonin Arewa maso yamma sun nemi agajin majalisar dinkin duniya. Hoto: Dikko Radda Women Support Group
Asali: Facebook

Gwamnonin sun nemi taimako ne domin magance matsalolin tsaro da farfaɗo da tattalin arzikin yankin.

Kara karanta wannan

Kotun Ingila ta yanke wa ɗan Najeriya hukunci bisa laifin kashe matarsa

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa gwamnonin sun nemi taimakon saboda yadda rashin tsaro ya jefa al'ummar yankin cikin tasko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalolin yankin Arewa a yau

Malam Dikko Umaru Radda ya bayyanawa jami'an majalisar dinkin duniya cewa yankin yana fama da matsaloli da dama, rahoton Arise News.

Cikin matsalolin akwai rashin tsaro, talauci, yawan yaran da ba su zuwa makaranta, shaye-shaye, yawan mutuwa yayin haihuwa da rashin aikin yi.

Yadda rashin tsaro ya shafi noman Arewa

Har ila yau Malam Dikko Radda ya bayyana cewa kashi 80% na mutanen yankin sun dogara ne da aikin noma domin samun abinci da kudin kashewa.

Amma matsalar tsaro, zaizayar kasa da dumamar yanayi sun fara barazana ga ayyukan noma a yankin a halin yanzu.

Jawabin jami'in majalisar dinkin duniya

Jami'in majalisar dinkin duniya da ya karbi gwamnonin a Abuja ya nuna farinciki ga yadda suka bayyana matsalolin yankin tare da alkawarin ba su taimako na musamman.

Kara karanta wannan

Kwamishina ya umurci 'yan sanda da ’yan banga su ceto ma’aikatan Dangote a Edo

Ya kara da cewa duk yunkurin majalisar dinkin duniya na yaki da talauci a Najeriya ba zai samu nasara ba har sai ya samu goyon bayan yankin Arewa maso yamma.

'Yan daba sun fitini mutanen Kano

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da gwamnatin Kano ke kokarin dakile matsalar 'yan daba, Gwamna Abba Kabir ya fusata kan sakin wasu da aka yi.

Gwamnan ya nuna bacin ransa inda ya ke zargin jam'iyyun adawa da hannu a sakin matasan bayan ya yi kokarin kawo karshen matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel