Tinubu Ya Ba Tsohon Gwamnan Zamfara da Sakataren Gwamnatin 'Yaradua Mukamai

Tinubu Ya Ba Tsohon Gwamnan Zamfara da Sakataren Gwamnatin 'Yaradua Mukamai

  • Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Alhaji Yayale Ahmed ya samu mukami a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
  • Tinubu ya ba Yayale Ahmed mukamin shugaban kwamitin gudanarwa na Jami'ar Ahmadu Bello da ke garin Zaria
  • Hakan ya biyo bayan nadin mutane 555 a kwamitin gudanarwa da mambobinsu a manyan makarantu 111 a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin shugabanni da mambobin gudanarwa a manyan makarantun Najeriya.

Tinubu ya naɗa akalla mutane 555 a manyan makarantun Najeriya guda 111 da suka haɗa da Jami'o'i da Kwalejin Fasaha da kuma na ilimi.

Tinubu ya gwangwaje Shinkafi da Yayale Ahmed da mukamai
Bola Tinubu ya nada Mahmud Aliyu Shinkafi da Yayale Ahmed muƙamai a Jami'o'nin ABU da UNIJOS. Hoto: Mahmud Aliyu Shinkafi, Asiwaju Bola Tinubu, Yayale Ahmed.
Asali: Facebook

Tinubu ya naɗa mutane 555 mukami

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ba Farfesa Attahiru Jega babban mukami a gwamnatin tarayya

Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Bayo Onanuga shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yau Asabar 18 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onanuga ya wallafa jerin sunayen wadanda suka samu mukamin har guda 555 daga manyan makarantu 111 a Najeriya.

Daga cikin wadanda suka samu mukamin akwai tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Alhaji Yayale Ahmed.

Yayale Ahmed da Shinkafi sun samu muƙami

Yayale Ahmed ya samu mukamin shugaban kwamitin gudanarwa na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna.

Sauran mambobin da ke karkashinsa sun hada da Opeyemi Aisha Oni da Hon. Rufus Bature da Hon. Rufus Bature da Hon. Wumi Ohwovoriole da Hon. Matthew Raymond Akpan.

Har ila yau, an nada tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahmud Aliyu Shinkafi a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na Jami'ar Tarayya da ke Jos a jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada tsofaffin gwamnoni 4 da Ministan Buhari a manyan muƙamai

Shinkafi zai jagoranci kwamitin da mambobinsu kamar haka Malandi Adamu Sabo da Chijioke Paul Okeifufe da Ayo Afolabi da kuma Mohammed Dharr Abdullahi.

Majalisar Dinkin Duniya ta yabawa mulkin Tinubu

A wani labarin, Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da salon mulkin shugaban kasa, Bola Tinubu a wasu ɓangarori masu muhimmanci.

Majalisar ta ce tabbas Tinubu ya yi namijin kokari wurin inganta fannini tattalin arziki da kuma samar da tsaro da ya addabi al'umma.

Mataimakiyar Sakataren Majalisar, Hajiya Amina Mohammed ita ta bayyana haka yayin wani taro a Abuja inda ta ce gwamnatin ta kawo tsare-tsare masu kyau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.