Niger: Kotu Ta Raba Gardamar Ka Ce Na Ce Game da Aurar da Mata Marayu 100

Niger: Kotu Ta Raba Gardamar Ka Ce Na Ce Game da Aurar da Mata Marayu 100

  • Yayin da ake kai ruwa rana kan aurar da ƴan mata 100 a jihar Niger, kotu da ke zama a Abuja ta dauki mataki kan lamarin
  • Babbar kotun Tarayya ta dakatar da shirin gudanar da auren da aka shirya a karshen wannan watan Mayun da muke ciki
  • Hakan ya biyo bayan maka kakakin Majalisar Niger, Abdulmalik Sarkin-Daji da Ministar harkokin mata ta yi domin tsaida shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan shirin aurar da mata marayu 100 a jihar Niger.

Kotun tarayya ta dakatar da shirye-shiryen gudanar da bikin bayan shigar da korafi da Ministar mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta yi.

Kara karanta wannan

"Babu ja da baya": Limaman Musulunci sun ɗaga yatsa ga Ministar Tinubu kan aurar da mata 100

Kotu ta yi hukunci kan aurar da mata 100 a jihar Niger
Kotu ta dakatar da shirin aurar da mata marayu a jihar Niger. Hoto: Uju Kennedy-Ohanenye, Abdulmalik Sarkin-Daji.
Asali: Facebook

Niger: Kotu ta dakatar aurar da marayu

Har ila yau, kotun ta ba Minista Uju ikon dakatar da shirin gudanar da auren da aka shirya a karamar hukumar Mariga, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan daukar nauyin aurar da matan da kakakin Majalisar jihar Niger, Abdulmalik Sarkin-Daji ya yi, cewar AIT News.

Sai dai Ministar ta ce hakan bai dace ba tare da maka kakakin Majalisar a kotu domin dakatar da shirin.

Uju ta ce ya kamata a duba yanayin ƴan matan a gaba domin inganta musu rayuwa wurin ci gabansu.

Daga bisani Uku ta yi alkawarin cewa ma'aikatarta za ta dauki nauyin karatun ƴan matan da kuma koya musu sana'o'i.

Kakakin Majalisar ya janye kudurinsa a Niger

Bayan matakin Ministar, Sarkin-Daji ya janye kudurinsa na daukar nauyin aurar da ƴan matan da aka shirya a karshen wannan wata.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da binciken TETFund, an fitar da N1bn a sharewa dalibai hawaye a makarantu

Sarkin-Daji ya ce daman ya yi hakan ne domin tallafa musu ganin cewa su marayu ne da suka rasa iyayensu saboda hare-haren ƴan bindiga.

Limamai a Niger sun kalubalanci Ministar Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa, Kungiyar limaman Musulunci a jihar Niger sun sha alwashin aurar da mata marayu 100 da aka yi niyya.

Limaman da sauran kungiyoyin addini sun yi fatali da korafin Ministar harkokin mata kan shirin aurar da yaran a karamar hukumar Mariga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel