Sabon Shugaban Senegal, Faye Ya Sanya Labule da Tinubu a Fadarsa, Bayanai Sun Fito
- Matashin sabon shugaban kasar Senegal, Bassirou Faye ya kawo ziyara Najeriya kasa da watanni biyu a kan karagar mulki
- Faye ya iso fadar shugaban kasar Najeriya da misalin karfe 3:09 da ranar yau Alhamis 16 ga watan Mayu a birnin Abuja
- Wannan na zuwa ne bayan rantsar da shugaban mai shekaru 44 a watan Afrilu bayan lashe zaben shugaban kasa a Senegal
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Sabon shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya iso fadar shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu a Abuja.
Bassirou Faye ya ziyarci Bola Tinubu a karon farko tun bayan hawa karagar mulki a farkon watan Afrilun wannan shekara.
Faye ya kawowa Tinubu ziyara karin farko
Matashin shugaban ya iso fadar Aso Rock da misalin karfe 3:09 a yau Alhamis 16 ga watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bassirou mai shekaru 44 ya kafa tarihi a kasar inda ya kasance mafi karancin shekaru a jerin shugabannin Sanagal.
Idan an tuna, Faye ya samu 54% na kuri'un da aka kada a zaben kasar da aka gudanar a watan Maris din wannan shekara.
Faye ya samu tarba daga Tinubu
Hadimin shugaban a bangaren kafofin sadarwar zamani, Dada Olusegun ya tabbatar da haka a shafinsa na X.
Olusegun ya ce tuni aka riga aka shirya tarbar sabon shugaban kasar a fadar Aso Rock cikin kayatarwa.
"Fadar shugaban kasa a Abuja cike ake da murna da kuma shirye-shiryen tarbar shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye a fadar Aso Rock."
- Dada Olusegun
Faye shi ne shugaban kasar Senegal na biyar da aka zaba wanda aka rantsar da shi a ranar 2 ga watan Afrilun 2024.
Tinubu ya tallafa a aikin hajji
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ba da tallafi domin rage tsadar kujerun aikin hajjin bana.
Mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima shi ya tabbatar da haka a jiya Laraba 15 ga watan Mayu a birnin Kebbi.
Shettima ya ce Tinubu ya tallafa da kudin ne domin rage wa maniyyata tsadar kujerar inda ya ce ya himmatu wurin inganta Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng