Gwamnatin Tinubu Ta Raba Tallafin Kayan Noma a Kano Domin Magance Yunwa

Gwamnatin Tinubu Ta Raba Tallafin Kayan Noma a Kano Domin Magance Yunwa

  • Gwamnatin tarayya ta fara raba tallafin noma ga wasu manoma a jihar Kano a wani yunkuri na wadata Najeriya da abinci cikin sauki
  • Shirin da ya gudana a karamar Hukumar Garun Mallam zai tallafawa manoma a shiyyoyin Kano uku da taki na ruwa da injininan huda
  • Aliyu Ibrahim Usman ya bayyana cewa wannan somin tabi ne a tsarin taimakawa manoma daga gwamnatin tarayya ta ma’aikatar albarkatun noma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Gwamnatin tarayya ta raba kayan noma ga wasu daga manoman da ke jihar Kano, a wani yunkuri na wadata Najeriya da abinci yayin da ake fama da karancinsa.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Karancin noma a Arewa na barazanar kawo matsalar abinci a Najeriya

Jami’in da ke kula da shirin gwamnatin tarayya na habaka noman daga ma’aikatar albarkatun noma ta kasa, Aliyu Ibrahim Usman ya ce wannan ne daki na biyu na tsarin rake talauci da habaka arziki na gwamnatin Najeriya.

Manoma
An raba kayan tallafin noma ga manoman Kano Hoto; J Countess
Asali: Getty Images

This day ta wallafa cewa ana sa ran shirin da ya gudana a Kadawa da ke karamar hukumar Garun Mallam a Kano zai zama wani mataki na farko da za a tabbatar da habaka abinci a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An raba manoman Kano kashi 3

An raba manoman da za su amfana da tallafin gwamnatin tarayya zuwa kashi uku daga shiyyoyin jihar.

A cewar jami’in da ke kula da shirin, Aliyu Ibrahim Usman dukkanin kungiyar manoman uku za su samu injininan huda, da abun ban ruwa guda 25, sai taki na ruwa da sauran kayan da za su taimakawa nomansu.

Kara karanta wannan

Daurarru sun shaki iskar ’yanci da Gwamnatin Kano ta yiwa fursunoni Afuwa

Radio Nigeria a tattaro cewa babban dalilin samar da kayan noman shi ne daukar matakan da za su tabbatar da karuwar kayan abinci a Najeriya.

Aliyu Ibrahim Usman ya shawarci manoman su yi amfani da kayan da su ka samu yadda ya dace.

Gwamnatin Katsina ta tallafawa manoma

A baya mun ba ku labarin cewa gwamnatin jihar Katsina ta tallafawa manoma 2,040 da kayan noman rani a wano mataki na habaka noma.

Gwamnan jihar, Mallam Umaru Dikko Radda ne ya sanar da raba tallafin ga manoman da ke kananan hukumomin jihar ya kuma ce za su rika horar da manoman domin wadata su da abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel