Kamfanin Jiragen Saman Emirates Zai Dawo Jigilar Fasinjoji a Nigeria, Gwamnati Ta Magantu
- Bayan dakatar da aiki a watan Oktoba, 2022, kamfanin jiragen sama na Emirates ya sanar da cewa zai dawo jigilar fasinjoji a Nigeria
- Kamfanin Emirates ya bayyana ranar 1 ga watan Oktoba, 2024 a matsayin ranar tashin jirgin farko daga Dubai zuwa birnin Lagos
- Mataimakin shugaban kamfanin Emirates, Adnan Kazim ya mika godiyarsu ga gwamnatin Najeriya kan gudunmawar da aka basu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kamfanin jiragen sama na Emirates ya sanar da cewa zai dawo jigilar fasinjoji a Nigeria daga ranar 1 ga watan Oktoba, 2024.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, kamfanin Emirates ya ce zai dawo yin jigila a Lagos, inda zai rika kai fasinjoji zuwa Dubai da sauran kasashe 140.
Mataimakin shugaban Emirates, kuma babban jami'in kasuwanci, Adnan Kazim ya ce jigila daga Lagos zuwa Dubai ta na da tasiri a Nigeria, kamar yadda kamfanin ya wallafa a Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kamfanin zai rika yin jigilar da jirgi kirar Boeing 777-300ER. Jigir mai lamba EK783 zai bar Dubai zuwa Lagos, amma jirgi mai lamba EK784 ne zai bar Lagos zuwa Dubai a ranar.'
"Muna godiya ga gwamnatin Nigeria bisa hadin guiwar da muka yi wajen ganin mun dawo da jigilar jiragenmu, muna fatan fasinjoji za su yi maraba da dawowarmu."
- Adnan Kazim.
Gwamnati ta tattauna da kamfanin jirgin Emirates
A watan Oktoba, 2022 ne kamfanin Emirates ya dakatar da jigilar fasinjoji a Nigeria saboda gaza samun ribar $85m da take harin samu a kasar.
A ranar 19 ga watan Nuwambar 2023, FRCN ta ruwaito ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Festus Keyamo ya sanar da cewa kamfanin Emirates zai dawo da jigilar fasinjoji.
Amma ya dauki kamfanin zuwa ranar 15 ga watan Mayun 2024, inda Keyamo ya kara sanar da cewa Emirates ya fadi takamaiman ranar da zai dawo yin jigila, in ji rahoton Channels TV.
Tinubu ya bar Najeriya sau 12 a shekara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tun bayan da Shugaba Bola Tinubu hau kujerar mulki, ya yi tafiye-tafiye 20 a cikin watanni 12, inda ya ziyarci kasashe 14.
Mun tattaro bayani dalla dalla kan wadannan tafiye-tafiyen, jerin kasashen da ya ziyarta da kuma abubuwan da ya je yi a kasashen.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng