Daurarru Sun Shaki Iskar ’Yanci da Gwamnatin Kano Ta Yiwa Fursunoni Afuwa
- Babbar mai shari’a a jihar Kano, Dije Abdu Aboki ta sahale wa hukumar kula da gidajen gyaran hali ta saki fursunoni 5
- Matakin na zuwa ne a lokacin da hukumomi a jihar ke kokawa kan cunkoso a gidajen gyaran hali da ke jihar Kano
- Hukumar kula da gidjen yarin jihar ta bayyana cewa an saki fursunonin ne saboda dadewa da kuma rashin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Babbar mai shari’a a jihar Kano, Dije Abdu Aboki ta sanya hannu wajen sakin daurarru biyar da ke daure a gidan gyaran hali a Gwauron Dutse a wani yunkurin rage cunkosun gidajen yarin jihar.
Daga wadanda su ka shaki iskar ‘yanci akwai wadanda su ka shafe lokaci mai tsawo a gidan gyaran halin ba tare da an gurfanar da su gaban kotu ba.
Daily Trust ta wallafa cewa jami’in hulda da jama’a na hukumar da ke kula da gidan gyaran hali a Kano, Musbahu Lawan Nassarawa ya bayyana cewa wasu daga daurarrun da aka saki su na fama da rashin lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shawara ga wadanda aka saki daga gidan yari
Babbar mai shari’a Dije Abdu Aboki ta shawarci daurarrun da gwamnati ta yafewa kan yadda za su gudanar da rayuwarsu.
Ta bayyana cewa kamata ya yi su ribaci wannan ‘yancin da su ka samu wajen zama ‘yan kasa na gari bayan sun shafe lokaci mai tsawo a daure.
Mai shari’a Dije Aboki ta kuma gargade su da su guji aikata dukkanin ayyukan da za su mayar da su kurkuku, kamar yadda Nigerian Tribune.
A na shi bangaren, shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali a Kano, Suleiman M Inuwa, ya godewa mai shari’ar bisa matakin afuwa da aka yi wa wadanda ake zargin.
Ya kara da yin bayanin cewa an sake su ne saboda dadewa da su ka yi a gidan ba tare da an fara sauraren shari’arsu ba, kuma da yawansu ba su da lafiya.
Cunkoso a gidan yari da ke Kano
A baya mun kawo mu ku labarin cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce akwai daurarru kimanin 400 da ba su san makomarsu ba a gidan yarin Kurmawa da ke jihar.
Kwamishinan ‘yan sanda, CP Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana hakan, inda ya ce da yawa daga takardar tuhumar daurarrun sun yi layer zana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng