Tsohon Sanata a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Yana da Shekaru 98
- Sanata a jamhuriya ta biyu a Najeriya, Michael Onunkun ya rasu yana da shekaru 98 a duniya a jiya Laraba 15 ga watan Mayu
- Marigayin ya rasu ne a daren jiya a asibiti da ke karamar hukumar Okitipupa a jihar Ondo bayan ya sha fama da jinya
- Ƴar marigayin, Morenike Alaka ita ta bayyana haka a yau Alhamis 16 ga watan Mayu inda ta ce sun tafka babban rashin jagora
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Tsohon sanatan a jihar Ondo, Michael Onunkun ya riga mu gidan gaskiya.
Sanata Onunkun ya wakilci tsohuwar jihar Ondo a Majalisar Tarayya a jamhuriya ta biyu.
Yaushe sanatan ya wakilci mazabarsa?
Marigayin wanda aka fi sani da MAE Onunkun ya rasu ne bayan fama da jinya mai tsayi yana da shekaru 98 a duniya, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onunkun ya wakilci Ondo ta Yamma a wancan lokaci wanda yanzu ta dawo mazabar Ondo ta Kudu daga 1979 zuwa 1983.
Ƴar Marigayin, Morenike Alaka ita ta bayyana rasuwar mahaifin nata a yau Alhamis 16 ga watan Mayu, Daily Post ta tattaro.
Alaka wacce tsohuwar shugabar karamar hukumar Okitipupa ne ta ce Onunkun ya rasu a daren jiya Laraba 15 ga watan Mayu a asibitin Okitipupa.
Ƴar sanatan ta fadi halin mahaifinta
"Mahaifina sanatan jamhuriya ta biyu yana da kurakuransa amma mutum ne mai karamci da son ilimi da kuma yara."
"Ya kasance ɗan siyasa nagari wanda a duk tsawon rayuwarsa ya ke siyasa kullum maganarsa kenan."
"Muna shirye-shiryen gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarsa a ranar 30 ga watan Satumba amma ya rasa ransa jiya."
- Morenike Alaka
Marigayin ya rasu ya bar mata 2 da kuma ƴaƴa 12 da suka haɗa da maza bakwai da mata biyar.
Sanwo-Olu ya tafka babban rashi a gwamnatinsa
A wani labari, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanar da mutuwar mataimakin shugaban ma'aikatansa, Gboyega Soyannwo.
Gwamnan Lagos ya ce mutuwar Gboyega ya yi matukar daga masa hankali inda ya ce marigayin kamar dan uwa ne a gare shi.
Asali: Legit.ng