Yan Ta’addan ISWAP da Boko Haram Sama da 40 Sun Mika Wuya a Jihar Borno
- Ƴan ta'addan kungiyoyin ISWAP da Boko Haram sama da 40 sun mika wuya ga rundunar sojin Najeriya a jihar Borno
- Jami'in yada labaran rundunar Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ne ya bada sanarwar a yau Alhamis a Maiduguri
- Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya kuma bayyana yadda mutanen suka mika wuya da irin abubuwan da suka zo da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Mutane sama da 40 ne da ake zargi na da alaka da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP suka mika wuya ga sojoji a jihar Borno.
Jami'in yada labaran rundunar sojin, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ne ya sanar da haka a yau Alhamis.
Rahoton da jaridar Daily Trust ta fitar ya nuna cewa mutanen sun hada da maza guda bakwai, mata tara da yara 31.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga ina tubabban Boko Haram suka fito?
Mutanen da suka shafe shekaru suna zaune da ƴan ta'addan sun dawo zama a yankunan Kwatan Turare da Doron Baga da ke karamar hukumar Kukawa a jihar Borno.
Sai dai Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya ce a binciken da suka yi sun gano cewa mutanen sun zauna da yan ta'addan ne a yankin Chadi.
Sannan daga baya suka samu kubuta daga wajensu, suka dawo yankunan Borno, cewar rahoton Daily Post.
Babban dan ta'addan Boko Haram ya sallama
Daga cikin mutanen da suka mika wuyan akwai kasurgumin dan ta'adda da ya shahara da kai hare-hare mai suna Mu'azu Adamu.
Mu'azu Adamu ya mika wuya ga sojin Najeriya ne tare da matarsa a yau Alhamis, 16 ga watan Mayu.
Boko Haram: Kayan da sojoji suka samu
Rundunar sojin ta sanar da cewa mutanen da suka mika wuyan an same su da kayayyakin aikin yau da kullum da dama
Rahotanni sun tabbatar da cewa daga cikin kayayyakin akwai riguna, bargon lulluba, kayan girki da dai sauransu.
A mika dalibar Chibok ga gwamnati
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Najeriya da ke karkashin rundunar operation hadin kai sun mika dalibar Chibok da suka ceto ga gwamnatin jihar Borno.
A ranar Alhamis ne kwamandan rundunar ya jagoranci bikin mika dalibar, Lydia Simon tare da ƴaƴan da ta haifa a hannun Boko Haram.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng