Atiku Ya Nemi Takawa Bola Tinubu Burki Kan Taba Kudin ’Yan Fansho Ayi Ayyuka

Atiku Ya Nemi Takawa Bola Tinubu Burki Kan Taba Kudin ’Yan Fansho Ayi Ayyuka

  • Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bayyana kudirin fara amfani da kuɗaɗen yan fansho domin yin ayyuka na gina kasa
  • Sai dai sabon tsarin ya fara samun suka daga masana da manyan yan siyasa ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa
  • Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya bayyana matakin da ya kamata a dauka a maimakon hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi martani ga gwamnatin Bola Tinubu kan karkatar da kuɗaɗen ƴan fansho.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya ce kuskure ne amfani da kudaden ya fansho da Bola Tinubu ke kokarin yi. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Za ayi ayyuka da kudin 'yan fansho

Gwamnatin ta bayyana kudurin amfani da kudaden yan fansho ne domin ayyuka na musamman wajen raya kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na tunanin kwashe kuɗin ƴan fansho ta yi wasu muhimman ayyuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai lamarin ya samu suka a wurin masana da yan siyasar Najeriya a cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Hukuma mai kula da kudaden ƴan fansho ta kasa ta sanar da cewa asusun kuɗaɗen fansho ya kai Naira tiriliyan 19.96

Me gwamnati za ta yi da kudin fansho?

Ministan kudi na kasa, Wale Edun ne ya bayyana cewa gwamnatin za tayi amfani da kudaden wajen yin ayyukan raya kasa.

A cewar ministan za a yi amfani da kuɗaɗen ne domin samar da wadatattun gidaje a Najeriya, cewar rahoton the Cable.

Jawabi daga masana harkokin kudi

Sai dai masana harkokin kudi sun nuna cewa tsarin dokar kasa bai ba gwamnatin damar amfani da kuɗin ma'aikata ba.

Wani masanin harkokin kudi, Musa Ibrahim ya bayyana cewa cikin abubuwan da doka ta ba gwamnati damar yi da kuɗaɗen yan fansho babu ayyukan da ga ke kokarin yi yanzu.

Kara karanta wannan

Kotun Ingila ta yanke wa ɗan Najeriya hukunci bisa laifin kashe matarsa

Matsayar Atiku Abubakar kan taba kudin fansho

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya soki kudurin gwamnatin na amfani da kuɗin wadanda suka yi ritaya.

A cewar Atiku Abubakar, ya zama wajibi ga gwamnatin ta samar da hanyoyin da za ta gudanar da ayyuka ba wai amfani da kuɗin ƴan fansho ba.

Ya ce lalle dole a tashi wajen gina tattalin Najeriya ta yadda za a samu damar yin ayyukan gina kasa.

Yan fansho sun nemi karin kudi

A wani rahoton kun ji cewa, tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan abinci na cigaba da addabar 'yan Najeriya daga bangarori daban-daban tun bayan cire tallafin man fetur.

Kungiyar 'yan fansho ta Najeriya ta nuna rashin jin dadinta bisa mawuyacin halin da mambobinta ke ciki ta kuma nemi a kara fansho mafi karanci zuwa N100,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel