Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke Dalibin ABU Zariya Bisa Zargin Cin Zarafin DPO

Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke Dalibin ABU Zariya Bisa Zargin Cin Zarafin DPO

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani dalibin jami’ar Ahmad Bello da ke Zariya bisa zargin keta mutuncin wani dan sanda
  • Ana zargin dalibin, mai suna Usman Adamu da laifin cin zarafi da batawa wani jami’in dan sanda suna a shafin facebook ba gaira ba dalili
  • Kakakin rundunar, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce ana ci gaba da zurfafa bincike domin tabbatar da gaskiyar abinda ya wakana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Bauchi- Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wani dalibin jami’ar Ahmad Bello (ABU), Usman Adamu mai shekaru 34 bisa zargin barazana da batawa wani jami’inta suna.

Kara karanta wannan

Matatar Dangote ta rage farashin mai ne saboda rashin inganci? Gaskiya ta fito

Ana zargin Usman da batawa baturen yan sanda a jihar, CSP Danladi Mohammed suna ta shafinsa na facebook.

Rundunar 'yan sanda
Rundunar 'yan sandan ta cafke dalibin ne bisa barazana ga jami'in dan sanda Hoto: Nigeria Police Force Bauchi State Command
Asali: Facebook

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil, a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na facebook ya ce wanda ake zargi ya yi rubutun karya masu dauke da barazana da tsoratarwa kan CSP Danladi Mohammed.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa sun nemi aukawa babban 'dan sanda

Rahotanni sun bayyana cewa wasu fusatattun matasa sun farwa, CSP Danladi Mohammed saboda bayanan da Usman Adamu ya wallafa.

A rahoton da Leadership News ta wallafa, ba dan wasu jami’an ‘yan sanda sun shiga tsakani ba, da tuni mahaifin matashin mai suna AbdulMumuni Liman ne ya shiga tsakani domin ceto baturen ‘yan sandan.

Sanarwar ta ce:

“Wani Abdulmumuni Liman, wanda aka fi sani da Kwakiya a kauyen Kyata dake yankin Burra ya kira wasu jami’an bijilanti da ake kira “Babeli” karkashin jaghorancin Yahaya Zomo daga karamar hukumar Toro zuwa kauyen Dangarfa.”

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

“Mai kara ya yi zargin Abdulmumuni Liman da ji masa muggan raunukan saboda sa’insa da suka samu kan wani fili.”

Ya bayyana cewa yanzu haka ana a ci gaba da zurfafa bincike.

Rundunar 'yan sandan Bauchi ta kama makamai

Ana da labari rundunar yan sandan jihar Bauchi, ta kame wasu bindigu da aka boye a karkashin kasa bayan samun wasu bayan sirri a kokarinsu na dakile rashin tsaro a jihar.

CP Auwal Muhammad Musa ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce daga samfurin bindigun da aka kama akwai ƙirar AK47 guda uku da AK49 guda ɗaya da kuma jigida guda tara da babu komai a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel