Hajji 2024: Jirgin Alhazan Farko a Najeriya Ya Tashi Zuwa Ƙasa Mai Tsarki

Hajji 2024: Jirgin Alhazan Farko a Najeriya Ya Tashi Zuwa Ƙasa Mai Tsarki

  • Tawagar alhazan farko a Najeriya sun lula zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana 2024 a ranar Laraba
  • Jirgin farko na alhazan ya tashi ne daga filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello a wani ɗan kwarya-kwaryar taro da gwamnan Kebbi ya halarta
  • Gwamna Nasir Idris ya godewa hukumar NAHCON bisa zaɓen jihar Kebbi a matsayin wurin da jirgin farko zai fara tashi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Jirgin alhazan farko daga jihar Kebbi ya tashi zuwa ƙasa mai tsarki kamar yadda aka tsara domin sauke faralin aikin hajji a wannan shekara 2024.

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ne ya tabbatar da haka a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na tunanin kwashe kuɗin ƴan fansho ta yi wasu muhimman ayyuka

Jirgin alhazai na farko ya tashi.
Tawagar alhazan farko da aka tsara za a fara ɗauka sun tashi zuwa Saudi Arabia Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Gwamna ya tabbatar da fara jigilar hajji

A sanarwar da gwamnan ya wallafa, ya ce an kaddamar da fara jigilar alhazan Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya a filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Idris ya ce:

"Wannan wata alama ce da ke nuna kudirin gwamnatin mu na ganin aikin hajjin bana 1445AH ya gudana cikin nasara tun daga farko har ƙarshe kamar yadda hukumar jin daɗin alhazai (NAHCON) ta tsara."

Hajji: Gwamna Idris ya godewa Tinubu, Shettima

Gwamnan ya kuma gode wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima bisa gagarumin goyon bayan da suka bayar a aikin Hajjin 2024.

A cewarsa goyon bayan da suke bayarwa don samun nasarar wannan aikin ibada ya ƙara nuna muhimmancin aikin a addinin Musulunci.

Nasiru Idiris ya kuma yabawa hukumar NAHCON bisa zaɓen jihar Kebbi a matsayim wurin da ta kaddamar da fara jigilar mahajjata zuwa ƙasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

"Tsohon gwamna Nyesom Wike ya tarawa Ribas Bashi," Simi Fubara ya fasa kwai

Ya kuma roƙi alhazan kar su manta su sanya Najeriya da shugabannin ƙasar nan a addu'o'in su.

"Ina rokon maniyyata suyi amfani da wannan dama mai tsada ta ibada su yi wa ƙasar nan, shugabanni da kansu addu'a.
"Mu haɗa kai wuri ɗaya mu tabbatar da aikin hajjin bana ya gudana cikin nasara kuma mu zama masu biyayya fiye da yadda ake tsammani."

- Gwamna Nasir Idris.

Tinubu ya bada tallafin N90bn a Hajji

A wani rahoton na daban, an ji Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tallafa da makudan kudi a harkokin aikin hajji saboda tsadar kujera a bana.

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima ya bayyana haka inda ya ce shugaban ya tallafa da N90bn domin saukakawa maniyyata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262